02
Feb
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar da ke fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa da kare hakkin ɗan adam ta SERAP, ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), a kotu kan karan kuɗin kiran waya, saƙon tes da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da ƙarin, wanda ya sa kuɗin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti ɗaya, yayin da kudin sayen data 1GB ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shi kuwa kuɗin aika saƙon tes ya tashi zuwa Naira 6 daga na huɗu da ake biya a baya.…