27
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (SGF), Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), watanni uku bayan ya yi murabus daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa zargin cewa an yi magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar. Lawal ya sanar da komawarsa jam’iyyar NDC a hukumance ne a Abuja ranar Talata, inda shugabannin jam’iyyar adawar suka tarbe shi gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Tsohon SGF ɗin ya kuma bayyana goyon bayansa ga tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar da ya ƙunshi Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, yana mai cewa…
