15
Sep
Ya ku matasan Nijeriya, Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ina rubuta wannan wasiƙa ne a gare ku a daidai lokacin da siyasar Nijeriya ke sake ɗaukar wani sabon salo, yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. A hankali, gangamin siyasa na fara ƙamari, ’yan siyasa na fara neman goyon bayan jama’a, ƙungiyoyi na fara bayyana matsayinsu, yayin da kafafen sada zumunta ke ƙara zama filin muhawara da yaƙin neman zaɓe. A irin wannan lokaci ne ya kamata mu, matasa, mu tsaya mu yi tunani sosai. Domin gaskiyar magana ita ce: siyasa ba ta da matsala; abin da…
