05
Sep
Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi zuwa tarukan Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar, a wani mataki da ya ƙara nuna muhimmancin da gwamnatinsa ke bai wa hulɗa da malaman addinin Musulunci da al’ummomin jihar. Gwamnan ya bar Fadar Gwamnatin Jihar Kano da misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda ya fara rangadin tarukan Mauludi daban-daban tare da ci gaba da ziyartar wurare har tsawon dare, kafin ya dawo Fadar Gwamnatin da misalin ƙarfe 7:02 na safiya. A cikin wannan rangadi na dare,…
