Abubuwan da ya kamata a sani kan ƙudirin ƙirƙirar ’yan sandan jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙudirin da ke neman a yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima domin bai wa gwamnoni damar naɗa kwamishinonin ’yan sandan jihohi a Nijeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi ƙasar.

Ƙudirin wanda ‘yan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen ‘yan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka. 

Dangane da sauya Kundin Tsarin Mulkin da aka yi la’akari da shi, kwamishinan ’yan sandan da gwamna zai naɗa a jiha zai jagoranci ‘yan sandan jihar a wani mataki da aka daɗe ana jira na ganin an raba ragamar hukumar ’yan sandan Nijeriya da ta kasa shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara kunno kai a ƙasar.

Ƙasar dai na fama da hare-hare daga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran munanan laifuka waɗanda kullum suke kai munanan hare-hare kan ‘yan ƙasa, waɗanda yawancinsu ake garkuwa da su, ana kashe su, ko kuma nakasa su.

Ko da yake hukumomin ‘yan sanda sun fara gudanar da ayyukan tsaro daban-daban tare da tura ƙarin jami’ai a faɗin ƙasar don magance matsalar rashin tsaro, har yanzu ba a samu raguwar aikata laifuka ba yayin da ‘yan bindigar ke gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci a garuruwa da ƙauyuka da dama.

Dokar wadda mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, da wasu mutane 14 suka ɗauki nauyi mai taken, ‘Ƙudirin dokar da za ta sauya Kundin Tsarin Mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 domin samar da kafa ‘yan sandan jihohi da al’amura masu alaƙa’ ta samu karɓuwa.

A cikin Kundin Tsarin Mulki na 1999, aikin ‘yan sanda yana cikin jerin dokoki na musamman don haka, ƙarƙashin ikon Gwamnatin Tarayya kai tsaye za a iya sauya hakan.

Da yake jagorantar muhawara kan ƙa’idojin ƙudurin dokar, mai ba da tallafi kuma memba mai wakiltar mazacar Ilorin ta Yamma/Asa, Tolani Shagaya ya bayyana cewa babbar manufar gwamnati kamar yadda yake qunshe a sashe na 14 (2) (b) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan, babban aikin Tarayyar Nijeriya, 1999, ita samar da tsaro da jin daɗin ‘yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, an fuskanci ƙalubale sosai a harkar tsaron ƙasa baki ɗaya, inda ya ce a dalilin haka, ‘yan sandan jihohi sun zama babu makawa a samar da su don qara ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ganin ƙasar nan ta kasance lafiya ga kowa da kowa.

Da yake ƙarin haske kan wasu muhimman sabbin abubuwan da ke cikin ƙudirin, ya ce, “matakin zai bai wa jihohi damar gudanar da aikin ‘yan sanda yadda ya kamata; ɓullo da cikakken tsari don tabbatar da haɗin kai tare da yin aiki babu riƙon sakainar kashi tsakanin ’yan sandan tarayya da ’yan sandan jihohi; samar da tsauraran matakan kariya da ke hana jami’an ’yan sandan tarayya katsalandan cikin harkokin ‘yan sandan jihohi ba tare da wani dalili ba, tare da jaddada haɗin kai da shiga tsakani a ƙarƙashin ingantattun batutuwa”.

Shagaya ya ci gaba da zayyana wasu muhimman tsare-tsare na ƙidirin da suka haɗa da kafa kwamitocin aikin ’yan sanda na jihohi daban-daban da hukumar kula da ayyukan ’yan sanda ta tarayya da ke da fayyace ayyuka da hukunce-hukunce, sake daidaita majalisar ‘yan sanda ta ƙasa har da shugabannin jihar.

Gyaran tsarin ya kuma tanadi cewa naɗin kwamishinan ’yan sandan jiha da gwamna zai yi zai kasance bisa shawarar hukumar ‘yan sandan tarayya da kuma amincewar Majalisar Dokokin jihar.

Sai dai gwamnan na iya tsige kwamishina bisa shawarar hukumar ’yan sandan tarayya, kuma bisa amincewar kashi biyu bisa uku na Majalisar Dokokin jihar.