Laifin fyaɗe: Kotu ta yanke wa Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne wata kotu a ƙasar Sifaniya ta yanke wa tsohon ɗan wasan Brazil Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi bayan samunsa da laifin yi wa wata budurwa fyaɗe a wani gidan rawa na Barcelona a watan Disamban 2022.

Wata sanarwa da kotun Barcelona ta fitar ta ce “Wadda abin ya shafa ba ta yarda ba.”

Masu gabatar da ƙara sun buƙaci da a yanke wa ɗan wasan da ya lashe gasar zakarun Turai hukuncin ɗaurin shekaru tara a gidan yari, sai kuma na shekaru 10 na gwaji.

Ɗaya daga cikin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da suka yi fice a duniya wanda ya taka leda a Barcelona da Paris Saint-Germain a lokacin da ya ke taka rawar gani, Alves, mai shekara 40, an gurfanar da shi a gaban kotu a farkon wannan watan kan zargin yi wa wata mata fyaɗe a gidan rawa na Sutton da sanyin safiyar ranar 31 ga Disamba, 2022.