‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi awon gaba da 20 a Neja

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Neja sun kai hari a yankin Basa da ke hayin Ƙaramar Hukumar Shiroro a jihar da safiyar Alhamis, inda suka kashe mutum biyu.

Majiyarmu ta ce sun kuma tagayyara mutum guda sannan sun yi awon gaba da aƙalla mutum 20.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyarmu cewa, kusan makonni biyu ke nan da ‘yan bindingar ke cin karensu ba babbaka a yankin inda suke kashe mutane, su kwashi dabbobi tare ƙona dukiyoyin jama’a.

Majiyar ta ƙara da cewa, a halin da ake ciki wanda aka raunata sakamakon harin yana asibiti yana karɓar magani.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Hon. Akilu, ya tabbatar wa majiyar tamu faruwar lamarin.

Jihar Neja ba ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga suka kafa wa ƙahon zuƙa a shiyyar Arewa ta Tsakiya.