Kakakin Majalisar Jihar Zamfara na fuskantar barazanar tsigewa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Moriki, na fuskantar barazanar tsigewa daga mafiya rinjayen mambobin majalisar.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, MANHAJA ta tattaro cewar galibin ‘yan majalisar na gudanar da taro a harabar majalisar da yammacin ranar Alhamis kan yadda za su tsige kakakin majalisar.

Kazalika, ziyarar da wakilinmu ya kai harabar majalisar ya gano yadda aka rufe harabar majalisar da kuma girke jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan danda da sibul difens a cikinta.

Bincike ya nuna hatta sandan majalisar bai tsira ba, don kuwa an samu wasu da suka yi awon gaba da shi.

Sai dai har zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren hukuma kan batun.

By Editor