Daga BASHIR ISAH
Mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya dawo Nijeriya.
Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
Koiki ya ce Igboho ya dawo Nijeriya ne don halartar jana’izar mahaifiyarsa.
Idan za a iya tunawa tun a 2021 Igboho ya bar Nijeriya inda aka ɗauke shi zuwa Jamhuriyar Benin bayan da hukumar DSS ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
