Na yi bankwana da gasar iyo a bikin ‘Rigata’, inji Rahana jarumar gasar

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Rahana Ibrahim Bunzawa wacce ta lashe gasar iyo (Linƙaya) wato tsere cikin ruwa ta ce ta yi bankwana da wannan wasa na ruwa har abada.

Ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke ganawa da wakilinmu a garin Yawuri jim kaɗan bayan kammala bikin ‘Rigata’ da aka gudanar kwanan nan.

Ta ce wannan shi ne karo na biyu da ta ke lashe wannan gasar a jere kuma a duk lokacin da ta shiga ita ce samun nasara saboda haka ta yi bankwana da shiga gasar Rigata daga bana.

“Na soma shiga gasar tun ina da shekaru goma sha shida kuma yanzu inda da shekaru ashirin saboda haka ya isa haka.

“Ba wani abu da  ya tsorata ni illa dai ina so ne na yi aure amma ba don haka ba zan cigaba kuma ina kyautata zaton duk lokacin da na shiga gasar zan yi nasara saboda abinda na gada ne a wajen mahaifina, kuma ko bayan na yi aure idan mijina ya amince zan iya shiga,” inji ta.

Ta bayyana jin daɗinta bisa ga irin goyon baya da ƙwarin gwiwa da ta ke samu a wajen mahaifinta duk da kasancewar ita ce auta a wajensa.

Shi kuwa mahaifin Rahana Malam Ibrahim Bunzawa ya bayyana Rahana a matsayin jaruma saboda ta yi ƙoƙarin ta gaje shi a wajen iyo (nutso) duk da kasancewar ta mace  kuma ita ce auta a wajensa.

“Zan daɗe ina kewarta haka-zalika ina fatan na samu daga cikin jikokina don maye gurbinta a wani wasan Rigata.”