Tsohon soja mai kai wa ’yan ta’adda kayan sojoji ya shiga hannu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta kama wani tsohon jami’in sojan saman Nijeriya, bisa samunsa da hannu wajen samar da kakin soja ga ’yan bindiga da suka addabi Jihar Zamfara.

An bayyana sunan sa da Ahmed Mohammed, jami’in da aka kora, wanda a baya yana aiki a sansanin sojin sama da ke Kaduna, ya aikata wannan ta’asa ne bayan kotu ta gurfanar da shi bayan wani laifin da sojoji suka aikata da ba a bayyana ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan ACP Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa Mohammed ya haɗa kai da Mushiri Abubakar wajen raba kayan sojoji ga kungiyoyin masu aikata laifuka da suka haɗa riƙaƙƙen ɗan bindigar nan mai suna Bello Turji da kuma abokan sa.

A wani samame na baya-bayan nan, jami’an tsaro sun kama Mohammed da Abubakar suna jigilar tarin kayan sojoji da suka haɗa da riguna, takalma, huluna, rigar sanyi da bel daga Kaduna zuwa Zamfara.

Adejobi ya jaddada wajibcin tarwatsa irin waɗannan ƙungiyoyin da ke samar da makamai da alburusai ga ‘yan ta’adda domin daƙile ayyukansu na aikata laifuka.