’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

’Yan Majalisar Wakilai sama da 60 ne ke neman a yi wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya kwaskwarima zuwa tsarin da ke ɗauke da Fira Minista kamar yadda aka faro a ƙasar. 

A ƙarƙashin jagorancin Wale Raji, ɗan majalisar wakilai na jam’iyyar APC mai wakiltar Jihar Legas, sun nemi sauyi a Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.

Daga cikin hujjojinsu akwai rage yawan kashe kuɗaɗe wurin gudanar da mulki da samar da tsare-tsare.

Har ila yau, masu goyon bayan ƙudurin sun tabbatar da cewa sabon tsarin ba zai fara aiki yanzu ba, zai iya kai wa zaɓen shekarar 2031.

Ƙudurin ya na neman a yi gyaran fuska a Kundin Tsarin Mulkin ƙasar na 1999 har zuwa jihohi da ƙananan hukumomi.

Tsarin da suke buƙata shi ne mai ɗauke da Fira Minista da kuma shugaban ƙasa wanda aka fara tun bayan samun ‘yancin kai.

Tsarin dai shi ne wanda ke ɗauke da Fira Minista da kuma shugaban ƙasa wanda ba shi da wani iko mai ƙarfi a ƙasar musamman a siyasance.