Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Bankin Access ya ba da sanarwar naɗin Mis Bolaji Agbede a maysayin Babbar Jami’ar Zartarwar Bankin ta riƙon ƙwarya.

Wannan naɗin ya biyo bayan rasuwar tsohon Babban Jami’in Zartarwar bankin mai suna Dakta Herbert Wigwe. A ranar 9 ga watan Fabrairu, 2024.

Mista Wigwe ya rasu a haɗarin jirgi mai saukar ungulu tare da matarsa da ɗansa da kuma tsohuwar shugabar Kamfanin canji na Nijeriya, Abimboloa Ogunbanjo a ranar Juma’a.

A wani jawabi na shugaban kwamitin daraktocin bankin ya yi ranar 12 ga Fabrairu, 2024 ya bayyana cewa, wannan naɗin ya samu sahalewar Babban Bankin Nijeriya wato CBN.

Mis Agbede wacce take da digiri na farko a vangaren lissafi da sitatistik a jami’ar jihar Legas, sannan ta yi digirinta na biyu a ɓangaren kasuwanci a jami’ar Cranfield da ke ƙasar Ingila, ta fara aiki a Bankin na Access tun a shekarar 2003.

Daga nan ta riƙe muƙamai da dama har Allah ya kai ta ga wannan muƙami na Babbar jami’ar zartarwa a wannan mako da muke ciki.