Gwamnatin Tinubu ta tsayar da ranar ganawa da su Ɗangote kan tsadar siminti

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta kira taron gaggawa tare da kamfanoni masu samar da siminti domin tattauna tashin farashin siminti a ƙasa.

Kafar Nairametrics ta rawaito cewa, a halin yanzu farashin buhun siminti mai nauyin 50kg a sassan Legas ya kai N9,500.

Majiyar ta ƙara da cewa a watan Janairun da ya gabata, farashin buhun simintin bai wuce N6,000 zuwa N6,500 a nan Legas ɗin ba.

Tuni dai wasu ƙananan ‘yan kasuwa suka daina sayar da siminti don gudun abin da ka je ya dawo na hauhawar farashinsa.

Sai dai a matsayin wani mataki na ƙoƙarin daƙile hauhawar farashin simintin da sauran kayayyakinn gini, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce gwanati za ta gana da jiga-jgan ‘yan kasuwa masu samar da siminti domin tattauna mafita.

Ministan ya nuna damuwa kan yadda farashin siminti ya cilla sama duk da kasuwarsa da ake samu daga ɓangaren ‘yan kwangila da sauransu.

Sanarwa ta nuna za a yi wannan tattaunawar ne ya zuwa ranar Litinin, 19 ga 2024 a babban zauren taron Ma’aikatar da ke Mabushi, Abuja.

Kuma kamfanonin da aka gayyata zuwa wajen taron sun haɗa da Ɗangote Plc, BUA Plc, Lafarge da dai sauransu.