Daga BASHIR ISAH
Shugabannin ƙasashen Afirka ƙarƙashin Ƙungiyar Haɗi Kan Afirka (AU) sun zaɓi Shugaban Ƙasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani, a matsayin sabon shugaban AU na 2024.
Ghazouani ya gaji wannan kujera ne daga Shugaba Azali Assoumani na ƙasar Comoros, wanda ya yi riƙe shugabancin ƙungiyar a 2023.
’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya
Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya
An yi zaɓen a ranar Asabar, 17 ga Fabrairu yayin babban taron ƙungiyar karo na 37 wanda ke gudana a Addis Ababa, babban birnin Habasha.