An sake buɗe Sahad Stores a Abuja bayan shafe sa’o’i 24 a rufe

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPC), ta sake buɗe katafaren shagon nan na zamani, wato Sahad Stores, da ke yankin Garki a Abuja bayan rufe shi na kimanin sa’o’i 24.

MANHAJA ta kalato cewar, an ga harkoki sun ci gaba da gudana a shagon yayin ziyarar da aka kai yankin a ranar Asabar.

A ranar Juma’ar da ta gabata gwamnati ta garƙame shagon saboda rashin daidaito da gaskiya a farashin kayayyakinsa.

Hukumar FCCPC ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar cewa, bincikenta ya gano farashin da ke rubuce a jikin kayayyaki ya bambanta da abin da shagon yake karɓa daga hannun kwastominsa.

Ta ƙara da cewa, binciken ya shafi baki ɗaya rassan Sahad Stores da ake da su a faɗin Abuja, wanda kuma an yi hakan ne domin fahimtar yanayi da kuma samar da gyara a harkar cinikayya.

Mataimakin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi, ya ce an gayyaci mabobin hukumar gudanarwar na shagon domin su zo su kare kansu, amma suka ƙi amsa gayyata.

Da Ɗumi-ɗumi: Ghazouani ya zama sabon Shugaban AU

Gwamnatin Tinubu ta tsayar da ranar ganawa da su Ɗangote kan tsadar siminti

Ya ƙara da cewa, duba da fahimtar da aka samu da kuma ƙoƙarin da Sahad Stores ɗin ke yi wajen daidaita farashin kayayyakinsa, “ya sa FCCPC ta sake buɗe shagon a ranar 16 ga Fabrairu, 2024 da misalin ƙarfe 7:00 PM.”

Ya ce kamata ya yi ‘yan kasuwa su zamo masu gaskiya game da yadda suke sanya farashin kayayyakinsu domin bai wa masu saye damar yin ra’ayi kan abin da suke da buqtar saye musamman ma a irin wannan lokaci da ake fuskantar tsadar rayuwa.