‘Yan daba sun wargaza zaɓen fidda gwani a Edo

Daga BASHIR ISAH

Wasu ‘yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa harabar Lushville Hotel and Suites da ke yankin GRA, Benin, inda nan ne wurin da aka shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC don takarar gwamnan Jihar Edo.

An ce sun wargaza shirin tattara sakamakon zaɓen ne inda suka kai wa wasu masu faɗa a ji farmaki tare kuma da ji wa ‘yan jarida da dama rauni da farfasa musu kayan aiki.

’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya

An sake buɗe Sahad Stores a Abuja bayan shafe sa’o’i 24 a rufe

Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Dr. Stanley Ughoajah, ya ce a lokacin da lamarin ya faru sun tafi hutun rabin lokaci.

Bayanai sun nuna cewa, gabanin wargaza shirin tattara sakamakon zaɓen, Sanata Monday Okpekholo daga Edo ta Tsakiya shi ne ke kan gaba da yawan ƙuri’u.