Tinubu ya ɗauki tsauraran matakai kan tsaro da yunwa

*Gwamnoni za su yi ’yan sandansu
*Ya umarci shugabannin tsaro su dirar wa masu ɓoye abinci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A jiya Alhamis ne Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnoni suka amince da kafa ’yan sandan jihohi a ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ƙarshen wani taron gaggawa da shugaban ya kira a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Qasa a Abuja.

Ministan ya ce, za a gudanar da tarurruka da dama, domin gyara hanyoyin kafa ’yan sandan jihohi.

Ya ce, “Amma yanzu, akwai kuma tattaunawa kan batun ‘yan sandan jihohin. Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi na ta tunanin kafa ‘yan sandan jihohi.

“Haƙiƙa, yanzu za a cigaba da tattaunawa kan wannan, har yanzu akwai sauran ayyuka da yawa a wannan ɓangaren. Amma abin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka amince da wajabcin samu a jihohi.

“Yanzu, wannan babban canji ne. Amma kamar yadda na faɗa, akwai buƙatar a yi ƙarin ayyuka ta wannan hanya. Za a yi tarurruka da yawa tsakanin gwamnatoci daban-daban da ’yan ƙasa don ganin hanyoyin cimma wannan manufa.”

A ranar Litinin ce dai gwamnonin PDP suka gudanar da taro a Abuja, inda suka tattauna batutuwa, musamman waɗanda suka shafi matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki, wadda ta haifar da matsalar tsada da raɗaɗin tsadar rayuwa.

Gwamnonin jam’iyyar ta PDP sun yi kira da a kafa rundunonin ‘yan sanda na jihohi a ƙarƙashin wata doka da za ta hana yin katsalandan daga duka matakan gwamnati.

Gwamnonin sun buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen ɓullo da wasu shirye-shirye da za su haɗa da duka vangarorin gwamnati don samar da mafita mai ɗorewa.

Gwamnonin na PDP sun kuma sha alwashin ci gaba da taka rawar da ta dace domin samar da tsaro ga al’ummansu, abun da a cewarsa ya sa suka jaddada buƙatar kafa ’yan sandan jiha.

Taron ya kuma koka kan karyewar darajar kuɗin ƙasar wato naira, inda suka nemi hukumomin da abun ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.

Sai dai jihar Zamfara da ta Filato na daga cikin jihohin da jam’iyyar ta PDP ke mulki, kuma suke kan gaba wajen fuskantar matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a tsawon shekaru.

Lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da ta dukiyoyi.

A wani cigaban kuma, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara a Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da IGP Kayode Egbetokun da Daraktan DSS, Yusuf Bichi umarni kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen yaƙi da masu ɓoye abinci a ƙasa.

Kafin wannan umarnin na Shugaba Tinubu, ‘yan Nijeriya na fama da ƙarancin abinci ba wai don babu abincin ba, sai don wasu ‘yan kasuwa sun tara abincin sun ɓoye wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci a sassan ƙasar.

Sai dai a wani yunƙuri da gwamnatin ƙasar ta yi don yaƙi da wannan hali na ɓoye abinci, Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya ce Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da NSA kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen kawar da wannan mummunar al’ada.

Idris ya ce, “Da farko, an bai wa Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara a Harkar Tsaro da Babban Sufeton ‘Yan Sanda da Daraktan DSS, umarni kan su hada hannu da gwamnonin jihohi wajen yaƙi da masu voye kayan abinci”.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Shugaba Tinubu a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ƙara da cewa, “A daidai wannan lokaci da ake buƙata a fito da kayan abinci domin mu samu mu daidaita farashi don amfanin ‘yan kasa, a lokacin ne kuma ‘yan kasuwa suka bada himma wajen voye abincin don wahalar da ‘yan ƙasa ko kuma don neman ƙazamar riba.

“Don haka gwamnoni da Shugaban Ƙasa sun yi matsaya kan cewa hukumomin tsaro su haɗa kai da gwamnoni wajen kawo ƙarshen lamarin.

“Domin amfanin ‘yan ƙasa, an yanke shawarar babu buƙatar shigo da abinci daga ƙetare a daidai wannan loakaci. Nijeriya na da ƙarfin da za ta ciyar da kanta har ta kai ƙetare.”

Daga nan, Idris ya ce tsadar rayuwar da ake fuskanta yanzu na ɗan lokaci, don haka ya buƙaci ‘yan Nijeriya a ƙara haƙuri saboda a cewarsa, lamarin zai zama labari nan ba da daɗewa ba.