NSCDC za ta haɗa kai da ƙananan hukumomi wajen samar da tsro a Jigawa

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a kano

Hukumar tsaro ta Civil Defence ta Ƙasa reshen Jihar Jigawa, ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da ƙananan hukumomin jihar domin yaƙi da ƙalubalan tsaro a jihar.

Kwamandan rundunar, Mohammed Ɗanjuma ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci Majalisar Ƙaramar Hukumar Taura a ci gaba da rangadin da yake yi a tsakanin ƙananan hukumomi 27 da jihar ke da su.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Mohammed Ɗanjumma, ya ce sun kai ziyara ne da nufin neman haɗin kai dan ganin an tabbatar da tsaro ingantacce, a yankin Taura baki ɗaya.

A jawabansu mabambanta, shugaban ƙaramar hukumar Taura, Hon Baffa da Hakimi Alh. Nura Usman, sun yaba da ƙoƙarin da hukumar tsaron ke wajen sauke nauyin dabke kanta a yankin da ma ji baki ɗaya.

Tare da bai wa hukumar tabbacin samun goyon bayansu domin ƙarfafa mata wajen gudanar da harkokinta yadda ya kamata.

Haka nan, sun yi kira ga jama’ar yankin da bai wa hukumar cikakken haɗin kai don cinma nasara kan sha’anin yaƙi da matsalolin tsaro.