Akwai hanyoyin magance matsalar tsaro da yunwa, aiwatarwa ne matsala – Sarkin Musulmi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce jagororin Arewan Nijeriya sun san hanyoyin da za a magance matsalar tsaro da talauci da yunwa da suka addabi yankin, amma ba su yi a aikace.

Sarkin Musulmi ya shaida wa taron sarakuna da jagororin Arewa cewa yadda matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi da kuma talauci, musamman a tsakanin matasan Arewacin Nijeriya, babbar barazana ce ga ƙasar.

Da yake jawabin da taron da suka gudanar a Kaduna, Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa yanzu ’yan Nijeriya a fusace suke, saboda yunwa da talauci, ga kuma “durƙushewar harkokin samun kuɗi da sana’o’i, don haka babu yadda za a yi mu ce komai na tafiya daidai alhali talauci da rashin tsaro sun addabi jama’a.

“Na sha faɗa kuma zan ƙara maimaitawa, al’amura sun dagule a Arewa kuma wajibinmu ne a matsayin sarakuna da ke jagorantar miliyoyin al’ummar Arewa mu nemo mafita.

“Kuma, ba wai ba mafitar ba ce babu, amma abin da ya dace ne ba ma yi, saboda duk lokacin da muka zauna irin wannan taro, kowa na kawo shawarwari masu kyau, amma kowannenmu a cikin ɗakin taro muke watsar da abin da shawarwarin.

“Shi ya sa a taron muka gayyato ƙungiyar dattawan Arewa da saurasu domin ganin yadda za a magance matsalolin Arewa da ma ƙasar nan a aikace; Ga ɓangaren ilimi, ga na lafiya su ma sunan nan baya ga talauci da rashin tsaron,” in ji Sarkin Musulmi.

A nasa jawabin, gwamnan Kaduna, Uba Sani bisa wakilcin mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, ta ce samun tsaro babban ginshiqi ne wajen samun ci gaban Arewa.

Don haka idan so muke a samu ci gaban tattalin arziki, wajibi ne mu san na yi wajen kawo ƙarshen garkuwa da mutane da sauran nau’ikan ta’addanci da suka zama ruwan dare a yankin.

Uba Sani na ganin mafita ita ce haɗa kai a tsakanin al’umma da shugabanni da gwamnonin Arewa wajen magance matsalolin da ke hana wa yankin cigaba; musamman kafa cibiyar tsaro ta bai-ɗaya domin yaƙi da ta’adanci.

A vangarensa, shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, wanda daraktan hukumar na jihar Kaduna, Abdul Enenche, ya waklita ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen daƙile barazanar tsaro tun kafin a aikatasu.

Jami’in, wanda ya buqaci haɗin kai wajen yaɗar miyagu, ya kuma bayya cewa masu ba wa ɓatagari bayanai babbar matsala ce da ke buƙatar magancewa da haɗin kan masu ruwa da tsaki.