Rahoto

Rage adadin masu taimataka wa Shugaban Ƙasa zai shafi ayyukan gwamnati – Tinubu

Rage adadin masu taimataka wa Shugaban Ƙasa zai shafi ayyukan gwamnati – Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bayar da hujjar cewa ministocinsa 47 ne a majalisar ministoci, inda ya ce adadin ya nuna irin ayyukan da ake bukata domin tafiyar da gwamnati mai inganci. Shugaban ya nuna shakku kan rage yawan majalisar ministocinsa, yana mai cewa babu tabbacin hakan zai inganta ayyuka. Ya kuma bukaci shugabannin kungiyar Kiristoci ta Nijeriya da su yada sakon haquri da fata a tsakanin ’yan Nijeriya, yana mai gargadin cewa akasin haka na iya cutar da kasar nan ba tare da gyarawa ba. Tinubu, wanda ya jaddada rawar da shugabannin addinai ke takawa…
Read More
Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ba zai taba cin amanar mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba. Da ya ke jawabi ga magoya baya a Abuja, jim kadan bayan yanke hukuncin Kotun Koli da ta tabbatar masa da zabensa, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ba a zalunci al’ummar Kano ba. A cewar Gwamna Yusuf, “mu na godiya ga Allah da wannan gagarumar nasara da ya ba mu. Mu na kuma godiya ga jagoranmu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa…
Read More
 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Alhaji Ƙarami Isyaka Rabiu da ASUSS sun jagoranci kaddamar da littafin tarihin shahararrun sha’iri na Manzon Allah da sahabban sa da Ahalinsa wato Marigayi Abdulaziz Fadar Bege bayan rasuwar fadar bege shekaru 10 da suka wuce. Littafan biyu wanda fitaccen marubuci Malam Bilyaminu Abul-warakat Ayagi, wanda ya rubuta litattafai sama da 100 wanda kuma shi  ne ya rubuta litafin tarihin Marigayi Fadar Bege da kuma na sha’irin mawakin Manzon Allah wato Ambasada Dakta Hafizu Abdullah wanda Alhaji Karami Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ya kaddamar da sayen litattafan hudu akan Naira miliyan biyu domin qarfafa gwiwa…
Read More
Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi shugabannin kananan hukumomin shida da laifin yajin aikin da malaman makarantun firamare ke cigaba da yi a yankin. Wike, wanda ya yi wa ’yan jarida jawabi a ranar Talata a Abuja jim kadan kafin wani taron gaggawa da hukumomin tsaro, ya ce jami’an kananan hukumomin ba su cika aikin da aka dora musu ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Malamai ta babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 15 ga watan Janairu. Yajin aikin…
Read More
Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
Read More
Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Daga BASHIR ISAH Tsohon Minista kuma fitaccen malamin Islama, Farfesa Isa Pantami, ya sanar cewa an tara kudi Nairia miliyan 50 domin ceto da ‘yan matan zuri’ar Al-Kadriyar da ‘yan binbdiga suka yi garkuwa da su a yankin Abuja. Pantami ya ce wani amininsa ne ya ba da tallafin ragowar Naira miliyan 50 daga cikin miliyan 60 da ‘yan bindigar suka bukaci a biya, bayan da ya tattauna batun da shi. A cewar tsohon ministan, “Alhamdu lil Laah! A kashin kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga barayi. Amma tun da a bayyane yake mun rasa ‘yarmu Nabeeha…
Read More
Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Karamar Hukumar Nengere a Jihar Yobe, Hon. Salisu Yerima ya bayyana irin kokarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen samar da romon dimukradiyya ga al'ummar yankin tun bayan hawansa mulkin jihar a 2019. Hon. Yerima ya ce Gwamna Buni ya yi abin a yaba da irin jagorancinsa na cire kyashi wajen dorawa daga inda tsohon gwamnan jihar, kuma Ministan Harkokin 'Yan Sanda na yanzu, Sanata Ibrahim Geidam ya tsaya. Ya ce an samu nasarori masu tarin yawa da suka haifar wa jihar da mai ido, inda ya ce shirye-shiryen…
Read More
Yadda Muhammad Rili ya farfaɗo da darajar hukumar KADA a Kaduna

Yadda Muhammad Rili ya farfaɗo da darajar hukumar KADA a Kaduna

Daga SANI SHEHU LERE a Kaduna Sau da yawa mutane kan zabi hukumomin da inda so samu ne a kai su don yin aiki, ba don komai ba, sai don irin maikon da ake hange a cikinsu da saukin aiki. Zuwan Hon. Muhammada Rili Hukumar KADA, ta isa ta canza wa mutane irin wannan tunani, su gane cewa a she kowane ofishi na da irin nasa gwargwadon maikon amma sai in an samu mutumin da ya iya murza gabobin da maikon da zai iya fita. Ma'ana, mutum ke gyara ofis, ba ofis ne ke gyara mutum ba. A kasa da…
Read More
Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Muryar Nijeriya, Mallam Jibrin Baba Ndace, ya ce hukumar za ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen bai wa duniya labaran Nijeriya da Afirka. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan hukumar a ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar Media Trust da ke Abuja. Yayin da ya bayyana Nijeriya a matsayin kasar da ba ta cika dari bisa dari, ya ce akwai labarai masu kyau da yawa da za a fada game da Nijeriya. “A Muryar Nijeriya abin da nake yi tun lokacin da…
Read More
Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya rantsar da Mai shari'a Umar Abubakar a matsayin babban alqali da Khadi Sadiq Usman Mukhtar a matsayin Grand Khadi na jihar. Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ne ya kaddamar da bikin rantsarwar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi a ranar Litinin. Da yake gabatar da mutanen biyu ga gwamnan domin rantsar da shi, sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya kuma karanta sunayen shugabanni da mambobin hukumar da Parastatals da za a kaddamar. Bayan rantsuwar, Gwamna Nasir…
Read More