Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ba zai taba cin amanar mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba.

Da ya ke jawabi ga magoya baya a Abuja, jim kadan bayan yanke hukuncin Kotun Koli da ta tabbatar masa da zabensa, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ba a zalunci al’ummar Kano ba.

A cewar Gwamna Yusuf, “mu na godiya ga Allah da wannan gagarumar nasara da ya ba mu. Mu na kuma godiya ga jagoranmu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa qwazonsa na ganin cewa kuri’un da al’ummar Kano su ka kada ba a kwace musu ba.

“Hakika Kwankwaso jagora ne kuma mu na alfahari da shi. Za mu cigaba da yin biyayya kuma ba za mu taba cin amanarsa ba,” inji gwamnan.

Ya kuma gode wa Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima bisa nuna dattaku na kin saka baki a shari’ar, inda ya ce, hakan ya kara wa qasar da kuma dimokuradiyya kima a idon duniya.
Gwamnan ya kuma gode wa alqalan Kotun Koli bisa abinda ya kira da “adalci wajen ganin sun bai wa mai gaskiya gaskiyarsa. Hakan zai kara gyara harkar zabe da dimokuradiyya a kasar.

“Mu na matuqar godiya ga al’ummar Kano bisa wannan soyayya da ake nuna mana. In sha Allah za mu bijiro da ayyukan alheri da za su kara havvakar arziki da ci gaba a jiharmu. Mun gode muku sosai,” inji gwamnan.