An cafke wani limami tare da wasu mutun hudu da ake zargin matsafa ne dauke da sassan jikin mutum a jihar Legas.
An gano su ne dauke da kwarangwal na kan mutum da kuma wasu sassan jiki.
Majiyarmu ta ce mazauna yankin Adamo a Ikorodu ne suka gano wadanda lamarin ya shafa kafin daga bisani aka mika su ga ‘yansandan yankin.
Majiyar ta kara da cewa, limamin da aka kama din ya bayyana wa ‘yansanda cewa wani maigidansa yake yi wa aiki.
A cewar mazauna yankin da lamarin ya faru, a ranar Alhamis da ta gabata ne ‘yansanda sashen yaki da garkuwa da mutane a yankin suka tsare matsafan.
“Na san limamin sama da shekara biyar, kuma shi ne wand ke jan mu sallah a yankinmu, ya zama tamkar abin koyi a gare mu,” inji majiyar.
