*Mutane sun fara hijira a yankin Bwari
*’Yan bindiga sun kashe magidanci, sun sace ’ya’yansa 13
*An ceto wanda aka sace daga Abuja zuwa Kano
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Daga dukkan alamu al’umma sun sake fadawa cikin fargabar rashin tsaro a yankin kewaye da hanyar Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja biyo bayan yadda a kwana-kwanan nan masu garkuwa da mutane ke yi wa mutane dauki dai-dai.
Rahotanni sun nuna cewa, wasu magidanta mutane sun fara yin hijira daga yankin Bwari, wanda ke kan iyakar Abuja ta vangaren Jihar Kaduna tun bayan shigowar sabuwar shekarar nan ta 2024, bayan kashe wani magidanci da sace ’ya’yansa 13 da kuma kama wasu iyalai tare da kashe wasu daga cikinsu.
To, sai dai kuma jami’an na cigaba da bai wa al’umma hakuri su na masu ba su tabbacin kawo karshen matsalolin.
Idan za a tunawa, a ranar 12 ga Janairu, 2024, iyalan wata dalibar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, wato Nabeehah, wacce ta ke karshen shekarar karatunta, suka fuskanci harin masu garkuwa da mutane a lokacin da suka sace akalla mutane 23 a kauyen Kawu da ke yankin Bwari.
Bayan kwanaki kadan da sace su, aka kashe ta, sannan bayan karin wasu kwanakin aka sake kashe mutane uku a cikinsu; lamarin da ya sanya mutanen yankin fara arcewa zuwa garin Bwari, saboda tsoron sake dawowar masu harin.
Daya daga cikin mazaunan da suka yi hijira zuwa Bwari, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa wata kafar yada labarai cewa, yanzu mutane ba su iya bacci a yankinsu.
“Na yi gudun hijira na kwanaki yanzu. Yanzu babu nutsuwa a Abuja,” inji shi yana mai karawa da cewa, “matata da ni da ’ya’yanmu mun bar gida tun ranar 2 ga Janairu.
“Mun gudu ne, saboda sau hudu ’yan ta’adda su na yin garkuwa da mutane tsakanin Kirsimeti zuwa sabuwar shekara a yankin.”
Bugu da kari, wasu gungun ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindigar daji ne sun kashe wani magidanci mai suna Tijjani Ahmadu mai shekaru 53 tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa guda 13, wadanda galibi yara ne, wadanda kuma su na tafiya tare da shi a yankin Katari da ke kan hanyar zuwa Abuja a yankin Jihar Kaduna.
Dan uwan dan kasuwar dan asalin Jihar Edo, AbdurRasaq, a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Laraba, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Janairu, 2024, yayin da wadanda abin ya shafa ke hanyarsu ta koma wa Kaduna bayan sun ziyarci Warri a Jihar Delta.
AbdurRasaq ya ce, “sun zo ziyara ne domin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. ’Yan uwana da iyalansu sun zo ziyara. Amma ’yan bindiga sun far musu a lokacin da suke komawa Kaduna, inda su ke cikin motocin bas guda biyu. Mota kirar Bus ta farko ta bi ta kansu, amma bas ta biyu ta tsaya. Yayana da yara 13 suna cikin bas ta biyu. ’Yan fashin sun kwashe su duka.”
Ya ce, daga baya dangi suka samu labari bayan da yara suka kira waya a hannun masu garkuwar.
Ya ce, a cewar yaran, “an buga kan babban yayana kuma ya fadi (wanda ya kai ga mutuwarsa),” ya na mai karawa da cewa, “amma yaran 13 har yanzu suna tare da su. Sun fara tattaunawa da ’yan fanshin daga Naira Miliyan 200, amma yanzu mu na kan Naira Miliyan 50.”
AbdurRasaq ya ce, ya yi magana ta qarshe da masu garkuwa da mutanen ranar Talata.
“Mun gano gawar dan uwana a ranar Asabar kuma muka binne shi washegari, 7 ga Janairu,” inji shi.
Ya ce, dangin ba za su iya tara Naira Miliyan 50 ba, yana mai cewa, “wannan kudi ne mai yawa.”
Daya daga cikin iyayen yaran da ta buqaci a sakaya sunanta ta ki yin wani karin bayani, ta ce, “ba yanzu ba, mu na cikin damuwar halin da yaranmu ke ciki a hannun masu garkuwa.”
Sai dai Zainab, matar Marigayi Ahmadu, wacce ta tabbatar da kashe mijin nata, ta ce, dangin na neman taimako a kan lamarin.
“Sun kashe mijina ne kuma sun tafi da, ’ya’ya 13,” Zainab ta shaida wa manema labarai a wata hira ta wayar tarho ranar Laraba, inda ta kara da cewa iyalan na neman addu’o’i da taimako daga duk wanda zai taimaka. “Mu na da ’ya’yanmu 13 a hannunsu,” inji ta.
Yayin da aka tuntuvi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, a ranar Laraba, don ya yi karin bayani kan wannan lamarin, sai ya ce, “zan tuntube ku.” Amma har zuwa lokacin hada rahoton nan bai kara cewa ce uffan ba.
A wanu labarin kuwa, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kaduna ta ceto wani mutum mai suna Segun Akinyemi da aka yi garkuwa da shi a Abuja kuma aka nufi Kaduna da niyyar kai shi Kano.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Kaduna, ASP Mansir Hassan, jami’an da ke aiki a hedikwatar Kawo, Kaduna, sun samu kiran da ake yi na sace mutane daga Abuja.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kuvutar da mutumin ne, wanda aka yi garkuwa da shi a Abuja babban birnin kasar ranar Laraba da yamma.
Rundunar ta ce, a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu ta samu rahoton yin garkuwa da wani mutum a Abuja, inda aka yi zargin masu garkuwar sun tafi da mutumin da suka sacen zuwa Jihar Kaduna.
Daga nan ne rundunar ta ce jami’anta suka riqa sanya idanu kan zirga-zirgar motocin da ke shiga jihar daga birnin na Abuja.
Sanarwar ta kuma ce da misalin karfe 1:00 na rana ne jami’nta suka tare wata mota qirar Toyota mai launin ruwan toka, wadda ke dauke da mutum hudu ciki har da direban, inda suka yi zargin masu garkuwar ne a ciki.
Yayin da mutanen suka ga ‘yan sanda sun tare su sai suka yi yunkurin tserewa, inda xaya daga cikinsu ya buxe wuta wa ‘yan sandan, wadanda su ma nan take suka mayar da martani.
Yayin da bangorin biyu suka bude wa juna wuta, lamarin da ya sa ‘yan sandan suka kubutar da wanda aka yi garkuwar da shi mai suna Segun Akinyemi da ke zaune a unguwar Area 3, Garki Abuja, tare da kama daya daga cikin masu garkuwar mai suna Chinaza Philip da ke unguwar Life Camp a Abuja, inda sauran mutum uku suka tsere, wadanda rundunar ta ce tana ci gaba da farautarsu.
Rundunar ta kuma ce ta kwato motar wadda ta mutumin da aka yi garkuwar da shi ne, da kuma kananan bindigogi nau’ikan Pistol da harsasai masu yawa daga wajen masu garkuwar.
Binciken farko ya nuna cewa maharan sun kama mutumin ne ranar Laraba 17 ga watan Janairu lokacin da ya fita daga gidansa da yamma.
Maharan na kan hanyarsu ta kai mutumin zuwa Kano a lokacin da ‘yan sandan suka kama shi.
