Abba na buƙatar addu’ar sauke nauyin al’ummar Kano – Dr. Salihun-nur Adam

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

An bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yana buqatar addu’ar milyoyin al’ummar Kano don ya samu damar sauke nauyin shugabancin da ya rataya a wuyansa.

A ranar Juma’ar makon jiya ne dai Kotun Ƙoli ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf da sahihancin nasararsa a zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Dakta Salihun-nur Adam wanda aka fi sani da Salihanur Shugaban Cibiyar Bincike akan Ganyayyaki da sauyoyi da tsire-tsire domin maganin cututukan da ke damun dan Adam dake Kano.

Haka kuma ya bayyana cewa, “zaman lafiya da aka samu daga zuwan Abba kamar hana kwacen waya da sauransu abun farin ciki ne kuma aikin gadojin sama biyu Tal’udu da Dan Agundi ga ayyukan lafiya wannan abin farin ciki ne kuma adalci a shari’ar nan ya kawo zaman lafiyar Kano, Nijiriya da Africa da ma duniya baki daya. 

“Kuma wannan ya nuna Tinubu dan dimokradiyya ne musamman rashin sanya baki da bai wa kotu damar yin aikinta kuma mun yi addu’ar kan faruwar hakan domin ina da mabiya a shafin sada zumunta kimanin miliyan 800 na yi tawassali da cewa in na taba aikin alkhairi ga wani dan Adam da Allah ya karba to ya sa mutanen Kano su yi nasara a kotu akan abin da suka zaba.

“Saboda haka akwai bukatar hakkuri da juriya ga gwamnan ga al’ummar Kano domin samun nasarar bunkasa kowanne fanni ga wannan gwamnati ta sa gaba musamman ilimi, lafiya da sauransu.”

By Editor