Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Alhaji Ƙarami Isyaka Rabiu da ASUSS sun jagoranci kaddamar da littafin tarihin shahararrun sha’iri na Manzon Allah da sahabban sa da Ahalinsa wato Marigayi Abdulaziz Fadar Bege bayan rasuwar fadar bege shekaru 10 da suka wuce.

Littafan biyu wanda fitaccen marubuci Malam Bilyaminu Abul-warakat Ayagi, wanda ya rubuta litattafai sama da 100 wanda kuma shi  ne ya rubuta litafin tarihin Marigayi Fadar Bege da kuma na sha’irin mawakin Manzon Allah wato Ambasada Dakta Hafizu Abdullah wanda Alhaji Karami Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ya kaddamar da sayen litattafan hudu akan Naira miliyan biyu domin qarfafa gwiwa ga marubucin wadannan littafai na masoya ma’aikin Allah wanda Kano ke kan gaba wajen aiki na alkhairi a kowane fanni kamar da yadda shi Alhaji Karami Sheikh Isyaka Rabiu ya bayyana a wajen wannan taro na kaddamar da littafan wanda aka yi karshen makon da ya gabata a Kano.

Haka kuma akwai shugaban Ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandare na Kasa reshen Jihar Kano ASUSS wanda shugaban ta Kwamared Abdullahi Usman Yalo ya jagoranci ayarin shugabannin kungiyar domin zuwa wannan gagarimin taro na zuwa wannan taro na kaddamar da wadannan litattfai biyu inda kungiyar ta Association Staff Union Secondary Schools ta ASUSS ta sai kwafi biyu akan kuzi Naira dubu 200 inda kuma Kwamared Yalo ya bayyana cewa indai maganar kaunar ma’aiki ne to malaman makaranta suna kan gaba wajen yin hidima ga Ma’aiki ta hanyar cusawa dalibai kaunar ma’aiki da kyawawan dabi’u da tarbiyya da sanin ya kamata ta hanyar koyar da su ta ingantacen ilimi ga dalibai maza da mata kamar yadda gwamnati ta dora musu amanar dalibai.

A karshe akwai Ambasada Garzali Yusuf Shugaban Kamfanin G Side Global wanda ya sayi kwafin littafin biyu akan Naira Dubu 200 wanda kuma ya bayyana farin cikinsa da ya kasance cikin masu wannan aiki na alkairi da ya shafi nuna kauna ga shugaban halitta, inda Alhaji Garzali ya ce za su ci gaba da wannan aiki na alkairi a iya tsawon rayuwarsa daga cikin dimbin mahalarta da suka yi jawabi akwai Shugaban Kwamitin taron Ado Ahmad Gidan Dabino, MON sai kuma Malam Ibrahim Mai Asshifa da Alhaji Aminu Abubakar Ladan Alanwaka da Malam Abubakar Shugaban Kamfanin yada labarai na Matashiya da sauran mahalarta maza da mata yara da manya daga sassa daban-daban na kasar nan.