Mu mayar da hankali ga yin gwaji kafin aure

Tare da ABBA ABUNAKAR YAKUBU

Zainab wata matashiya ce da ke koyon aikin jinya, kuma take daf da daidaita zancen aure tsakaninta da wanda take so ta aura. Sanin muhimmancin yin gwajin kwayoyin halittar jini ga aurenta, ya sa ta garzaya domin duba nau’in kwayar halittar jininta a wani asibiti da ke cikin garin Katsina.

Sai dai ga mamakinta sakamakon da ya fito ya tsoratata ganin cewa tana dauke ne da nau’in genotype mai AS, savanin abin da take sa rai ta gani na AA, wanda a cewarta akasari ‘yan gidansu ke da shi. Babu shakka wannan sakamako ya girgiza wannan matashiya ainun, wacce ke ganin kasancewarta AS zai iya sa ta rasa masoyinta ko wanda take shirin aure, idan har aka samu akasi ba AA ne da shi ba.

Ba da jimawa ba, matasan nan da suke yawan yada soyayyarsu a zaurukan sada zumunta, musamman manhajar Tiktok, Ahmed da Safeera, su ma labari ya watsu cewa soyayyarsu ba ta kai ga aure ba, saboda an gano dukkansu suna dauke da kwayar halittar jini nau’in AS.

 Kodayake wasu na zargin wannan ba shi ne maqasudin rabuwarsu ba, amma dai tabbas akwai batun rashin jituwar kwayoyin halittar jininsu. Wannan labari ya jawo cece-kuce da dama a zaurukan sada zumunta, saboda takaicin abin da ya raba wadannan masoya, da wasu ke sha’awar yadda suke bayyanawa duniya soyayyar da suke yi.

Irin wannan sakamako na bazata ya raba masoya da dama, musamman ma wadanda ke daf da aure, kamar Hauwa’u wata daliba da ke karatu a Jami’ar Jos, wacce ta bayyana min cewa, ta yanke shawarar komawa karatu ne, bayan da sakamakon gwajin da suka yi da saurayinta da za ta aura, wanda suka shafe tsawon shekaru 3 suna soyayya, inda aka gano dukkansu suna da nau’in jini na AS ne. Kuma har yanzu ta kasa sakin jiki ta yi wata soyayya da wani.

Ba kamar Hauwa’u ba, ita Fatima wacce har aure sun yi da wanda take so ba tare da yin gwaji ba, kwatsam sai bayan haihuwarta na farko suka gano yarinyar na dauke da cutar Sankarar Jini. A lokacin ne suka je suka yi gwaji suka fahimci kuskuren da suka yi a baya. Da yake Allah Ya kaddara ba za su jima tare ana wahalar jinyar ‘yar da suka haifa tare ba, sai Allah Ya dauke ran Shamsuddeen mijin Fatima ta sanadiyyar hatsarin mota. Don haka, yanzu da ta koma zawarci ta kuma fahimci hadarin aure ba gwaji, duk bazawarin da ya zo mata abin da take fara tambayarsa shi ne, “Mene ne genotype din ka, don ni nawa AS ne!”

Idan da a ce haka ‘yan mata da samari ko iyayensu ke yi na jaddada muhimmancin gwajin HIV da Genotype da an ceci rayuka da dama, kuma ba a jefa yara cikin azabar jinyar cutar Sikila ba.

Gwaji kafin aure wani sabon al’amari ne da ya shigo cikin al’ummarmu, wanda ake yi domin tabbatar da ingancin lafiyar ma’aurata kafin su yi aure. Duk da kasancewar canji ne da aka jima ana gwagwarmaya da jama’a don su karva, duba da irin kalubalen da ake fuskanta a dalilin rashin yin gwajin. Sai dai har yanzu ba ko’ina ne ake bai wa yin gwaji muhimmanci ba, don haka ne ma ake yawan samun matsaloli na cututtuka a tsakanin ma’auratan ko yaran da ake haifa.

Masana harkar lafiya sun dade suna fadakarwa kan muhimmancin yin gwajin jini da na kwayoyin halitta don sanin ko wani daga cikin ma’auratan na dauke da cutar kanjamau, ko kuma kwayoyin halittarsu ba su daidaita ba. Sannan har wa yau sanin nau’in rukunin jinin amarya shi ma abu ne mai muhimmanci, saboda yaran da za ta haifa.

Bincike ya nuna cewa, idan daya daga cikin ma’aurata yana dauke da cutar HIV mai karya garkuwar jiki, zai iya yada cutar ga abokin zamansa ta hanyoyin da likitoci suka tabbatar cutar na yaduwa. Domin ceton rayukan ma’aurata, da kula da muhimmancin lafiyarsu, wani jigo mai karfi daga cikin sharuddan aure a cikin koyarwar addinin Musulunci. Haka ma kuma abin yake a koyarwar addinin Kirista.

Rayuka da dama sun salwanta, ma’aurata sun samu kansu cikin tsananin jinya, da fuskantar kyama da wariya, sakamakon bayyanar cutar HIV a tsakaninsu bayan sun yi aure da wasu watanni ko makonni. Saboda rashin zuwa yin gwaji. Haka nan shi ma, gwajin kwayoyin halitta na genotype, yana da tasirin gaske a duk wani aure da za a kulla. Saboda rashin yin wannan gwaji da kiyaye shi, ke sa a rika haihuwar yara masu lalurar sankarar jini, wato Sikila.

Binciken masana kiwon lafiya na nuni da cewa, akwai nau’ikan kwayoyin halittar jini kimanin guda biyar zuwa shida da bincike ya tabbatar da su, da suka hada da AA, AS, SS, CC, AC, da SC. Kowanne dan Adam za a iya samun sa da daya daga cikin wadannan nau’ikan kwayoyin halittar, wadanda daga ciki akwai wasu da haduwar su take sa a haifi da mai lafiya, wasu kuma haduwar su ta haifar da da mai Sankarar Jini, saboda rashin jituwar kwayoyin halittar. Kamar misalin ruwa ne maiko, ko sinadarin makamashi irin su kanazir ko fetur. Dukkan su dai yanayin ruwa ne da su, amma halittar su daban-daban ne!

Likitoci suna cewa, idan ma’aurata masu nau’ikan halittar jini mai laqabin AA da AA, ko AA da AS, ko kuma AA da AC suka yi aure to, yaran su sun kuvuta daga cutar Sankarar Jini. Amma idan kwayoyin halittar su AS da AS ne, ko AS da SS, ko SS da AC, ko kuma SS da CC ne, ba zai yiwu su yi aure ba sam, don kuwa kwayoyin halittar su ba za su jitu da juna ba, za su iya haifar yara masu Sikila, wato Sankarar Jini, ko da kuwa ba dukkan su.

Yana da kyau jama’a su gane cewa, cutar Sankarar Jini cuta ce mai matukar hadari ga lafiyar dan Adam, wacce ke hana yara kuzari ko girma kamar sauran yara, kuma suna rayuwa cikin yawan laulayi da kwambarewar gabobin jiki. Kuma akasarinsu ma ba sa tsawon rai.

Kawo yanzu dai ba a gano takamaimen maganin wannan mugunyar cuta ba. Sai dai kokari da masana sirrin harhada magunguna ke yi na gano makarin wannan cuta. Shi ya sa likitoci ke ba da shawarar a daina gaggawar hada auren masoya mace da namiji da ke sha’awar aure, har sai an tantance nau’in kwayar halittar jininsu ta hanyar yin gwaji.

Saboda kalubalen da ake fuskanta wajen dakatar da auren da ake daf da daura shi bayan an gano rashin jituwar jinin ya kamata a ce tun lokacin da iyaye suka tabbatar da wanda za su bai wa ’yarsu, shi ma kuma namijin iyayen sa suka tambayar masa matar da yake so har suka hadu da iyayen ta aka tattauna tun a matakin farko to, tun kafin a kai ga matakin BADA SADAKI ko DAURA AURE a je a yi wannan gwajin, saboda babu wasu iyayen da za su ji dadi a ce sai an tara mutane an hadu don daurin aure a ce a fasa, saboda sakamakon da gwajin ya bayar.

Shawara dai ga iyaye a nan ita ce tun kafin tafiya ta yi nisa yaransu su shaku da juna, har rabuwar su ta iya zama da matsala to, a yi wadannan gwaje-gwajen, don sanin makamar alakarsu. Kada a bari sai abin ya kai wani matsayi da raba su zai zama da wahala, ko kuma ta kai matakin da za su ce tun da ba za su samu damar yin aure ba to, za su je su aikata abin da zai jefa su cikin fushin ubangiji. Ko kuma su masoyan su samu kansu cikin wata matsala da za su jefa rayuwar su cikin tsaka mai wuya!