Matsalar tsaro da tattalin arzikin Dala Tiriliyan 1

Manufar Gwamnatin Tarayya na samar da Dala Tiriliyan 1 na tattalin arzikin kasa ba zai yiwu ba idan har aka cigaba da samun tabarbarewar matsalar rashin tsaro a kasar. Mafita ita ce jami’an tsaro su gaggauta daukar mataki tare da tabbatar da cewa an fatattaki ’yan bindiga da sauran miyagun da ke ta’addanci a kasar. Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin leken asiri a wani taron tsaro da shugaban kasa ya gudanar kwanan nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar shugaban, yayin da ake samun cigaba tare da kawar da wasu matsalolin tsaro a sassa daban-daban na qasar, a karshe dai za a ayyana nasara ta hanyar kawar da barazanar rashin tsaro bakidaya ga ‘yan kasar. Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban kalubale a bangaren kokarin da gwamnati ke yi na bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya kuma jaddada cewa dole ne sojojin kasar su cimma burinsa na ganin cewa al’ummar kasar sun samu cigaba mai dorewa na samar da ganga miliyan biyu na danyen mai a kowace rana, ciki har da na’urar dakon man fetur a cikin rubu’in farko na shekarar 2024.

Kalaman na Tinubu na zuwa ne a ranar da ’yan ta’adda suka kashe akalla mutane 17 tare da yin garkuwa da wasu 58 a wasu kauyuka uku da ke karamar hukumar Kauru ta Jihar Kaduna; da wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe wani fasto na Cocin Christ In Nations (COCIN) a garin Kwari da ke karamar hukumar Geidam a Jihar Yobe a wani sabon barazanar ‘yan bindiga da ya barke a sassan kasar nan.

Hakazalika, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane bakwai ‘yan gida daya tare da kashe dan sanda guda. Rikicin ya kara nuna damuwa da rashin tsaro a Abuja da sauran sassan kasar.

Babu shakka, rashin tsaro ya zama hatsari a halin yanzu ga ‘yan Nijeriya da tattalin arzikinta. Hasashen kan tattalin arzikin kasar daga masana da hukumomin kasa da kasa, abin ya yi muni. Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) a cikin rahotonsa na ‘World Economic Outlook Update: Near-Term Resilience, Persistent Challenges (Yuli 2023)’, ya yi hasashen cewa cigaban tattalin arzikin Nijeriya zai ragu a 2023 da 2024 saboda matsalolin tsaro a fannin mai. Ta bayyana cewa, tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kashi 3.2 a shekarar 2023, kafin ya ragu zuwa kashi 3.0 a shekarar 2024.

IMF ta ce, “A yankin kudu da hamadar Sahara, ana hasashen cigaban zai ragu zuwa kashi 3.5 cikin 100 a shekarar 2023 kafin ya kai kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2024. Ana hasashen cigaban Nijeriya a 2023 da 2024 sannu a hankali zai ragu, daidai da hasashen watan Afrilu, wanda ke nuna tavarbarewar al’amuran tsaro a fannin mai.”

An riga an fara ganin tasirin rashin tsaro, cin hanci da rashawa da sauran munanan abubuwa masu ban tsoro yayin da sama da kamfanoni 15 na kasa da kasa suka bar Nijeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, a cewar bayanai daga kungiyar tuntuvar ma’aikata ta Nijeriya (NECA).

A wasu sassan kasar kuma, rashin tsaro ya gurgunta harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma. A shiyyar Arewa ta tsakiya manoma ba za su iya zuwa gonaki ba saboda rashin tsaro. Hakan ya haifar da karancin kayan abinci da tsadar kayan masarufi na gida. Rashin tsaro ya yi matukar ga samuwar jari daga waje kai tsaye. Yayin da kamfanoni da yawa ke barin kasar, ma’aikata da yawa suna rasa ayyukansu, kuma yawancin ‘yan kasa suna shiga cikin matsanancin talauci.

Jaridar Blueprint Manhaka na ganin cewa bai kamata a bar lamarin ya cigaba ba. Bai kamata Shugaban Kasa ya tsaya kawai yana korafin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasa ba. Ana bukatar yin wani abu mai tsauri kuma cikin gaggawa don dakile barazanar. Yakamata a karfafawa jami’an tsaro kwarin gwiwa tare da hada karfi da karfe domin murkushe masu hannu a cikin matsalar rashin tsaro. Babban aikin gwamnati shi ne samar da tsaro da jin dadin jama’a. Bai kamata gwamnatin tarayya ta rungume hannuwa ba. Wannan lokaci ne da za a murkushe ’yan bindiga, ’yan ta’adda da sauran miyagun da ke addabar ’yan kasa.