17
May
Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu yabo daga Hon. Sa’ad Ibrahim Darki, wanda aka fi sani da Janar, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa ilimi a jihar Kano. Hon. Sa’ad Janar ya bayyana cewa gina jami’ar Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUSTECH) Wudil a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003, da kuma jami’ar Northwest University a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu daga 2011 zuwa 2015, na daga cikin manyan dalilan da suka sa yake goyon bayan Kwankwaso. Ya ce Kwankwaso ya nuna kishin ilimi musamman ga ‘ya’yan talakawa,…
