A cikin wannan zamani da fasahar sadarwa ta zama ruwan dare, an shiga wani sabon yanayi da ke haifar da babbar matsala ga tarbiyya da mutuncin al’umma. Abin da a da ake ɓoye shi a cikin sirri da kunya, a yau ya koma ana ɗaukarsa a matsayin abin wasa ko soyayya ta zamani. Musamman yadda wasu ’yan mata ke tura wa samari bidiyon tsiraici, ko kuma hotunan da ba su dace ba, yana daga cikin abubuwan da ke rusa ginin tarbiyyar al’umma cikin gaggawa.
Wannan wasiƙa tana da manufar yin kira na musamman ga ’yan mata da maza baki ɗaya, domin tunatarwa da faɗakarwa kan girman wannan aiki da illolinsa a addini, rayuwa da kuma gobe.
Ga ‘yan mata: darajar ki ta fi komai:
Ya ke ‘yar uwa Musulma, ki sani cewa jikinki amana ce daga Allah (SWT). Ba abin wasa ba ne, ba kuma abin kasuwanci ba ne ko abin yin gasa a shafukan sada zumunta. Allah Ya yi ki da daraja, Ya kuma ba ki mutunci da bai kamata ki wulaƙanta shi ba.
Tura bidiyon tsiraici ko hotuna marasa kunya ga saurayi, ko da kuwa ana cewa soyayya ce, ko alƙawari ne, ko kuma an yi miki rantsuwa, dukkan su ba su halatta ba a shari’ar Musulunci. Sau da yawa abin da ake fara shi da soyayya, yana ƙarewa da nadama da kukan “da na sani”.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: “Ka ce wa muminai maza su runtse ganinsu, su kuma kiyaye farjinsu…” (Suratul Nur: 30)
Sannan Ya ƙara da cewa: “Ka ce wa muminai mata su runtse ganinsu, su kiyaye farjinsu, kada su nuna ado sai abin da ya bayyana…” (Suratul Nur: 31)
Wannan umarni ne kai tsaye daga Mahalicci, yana nuna muhimmancin tsare mutunci da kauce wa duk abin da zai jawo fitina.
Ya ke ’yar uwa, abin da kika aika a yau domin “soyayya”, zai iya zama abin wulaƙanci gobe idan soyayyar ta ƙare. Akwai matasa da dama da suka shiga damuwa, aka yi musu barazana da abin da suka aiko, aka kuma jefa su cikin kunya da ba su da mafita.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Ahlihi Wasallam) ya ce: “Al-haya’u shu’batun min al-iman”, wato Kunya reshe ce daga imani.
Idan kunya ta tafi, to imani yana rauni, rayuwa kuma tana shiga cikin hatsari.
Ga maza: ku ji tsoron Allah a idanunku da zuciyarku:
Ya ku samari da mazaje, Musulunci bai halatta ku nemi ganin tsiraicin wacce ba matarku ba. Idan mutum yana kallon abin da Allah Ya haramta masa, yana rage darajar zuciyarsa ne, kuma yana cusa mata cuta.
Allah Ya ce: “Kada ku kusanci zina; lalle ita alfasha ce kuma hanya ce mafi muni.” (Suratul Israa: 32)
Kallon haram, jin daɗin haram, da neman hotuna ko bidiyo na tsiraici duk suna daga cikin hanyoyin da ke kai mutum zuwa zina. Musulunci ba wai kawai ya hana zina ba ne, har ma ya hana duk hanyoyin da ke kaiwa gare ta.
Ya kamata kowane namiji ya tuna cewa yana da uwa, yana da ƙanwa, yana da ’ya’ya mata a gaba ko a yanzu. Idan ka ga hoton wata ‘yar mutane tana tsiraici, ka tambayi kanka: shin kana son a yi wa ’yar uwarka haka? Kana son a wulaƙanta mahaifiyarka haka?
Manzon Allah (SAWW) ya zo masa wani saurayi yana neman izini domin ya yi zina, sai Annabi ya yi masa nasiha mai girgiza zuciya, ya tambaye shi ko zai yarda a yi hakan da mahaifiyarsa, ‘yar uwarsa, ko ‘yarsa. Sai saurayin ya ce a’a, kuma Annabi ya ce haka nan mutane ma ba sa so. Daga nan ya yi masa addu’a Allah Ya tsare shi.
Wannan yana nuna cewa Musulunci yana gina tunani ne da tausayi, ba son kai ba.
Illolin wannan ɗabi’a a rayuwa:
Tura bidiyon tsiraici ko neman ganin sa yana da illoli masu yawa:
Na farko, yana rusa mutunci da darajar mutum. Sau da yawa bayan rabuwar soyayya, abin da aka aiko yana zama makami na wulaƙanci da cin zarafi.
Na biyu, yana haddasa damuwa da tashin hankali. Akwai mutane da dama da suka shiga damuwar rai (depression) saboda abin da suka aika ko aka fallasa.
Na uku, yana haifar da rashin amincewa a al’umma, musamman a tsakanin ma’aurata ko masu neman aure.
Na huɗu, yana iya kai mutum ga laifi da hukunci a shari’a ko doka, musamman idan an yaɗa hotuna ba tare da izini ba.
Gargaɗi da kira ga gyara:
Ya ku ‘yan uwa, wannan zamani na fasaha yana da amfani idan aka yi amfani da shi da kyau, amma yana iya zama fitina idan aka yi sakaci. WhatsApp, TikTok, Instagram da sauran kafafen sada zumunta ba wuraren rusa mutunci ba ne, wuraren gina al’umma ne idan aka yi amfani da su cikin tsoron Allah.
Musulunci ya koya mana cewa kowane aiki ana rubuta shi, ko da kuwa babu wanda ya gani a duniya. Allah yana gani, Mala’iku suna rubutawa.
“Kuma duk abin da kuka aikata, za ku same shi a wurin Allah, ko alheri ne ko sharri.” (Suratul Zilzal: 7-8)
Kammalawa: Kira zuwa ga tsafta da mutunci:
A ƙarshe, wannan wasiƙa tana kira ne ga ‘yan mata da maza da su koma ga Allah, su tsare mutuncinsu, su guji duk wani abu da zai iya jawo musu nadama a gaba.
Soyayya ba ta nufin wulaƙanta kai. ƙauna ba ta nufin karya dokar Allah. Rayuwa ba ta nufin bin sha’awa ba tare da tunanin sakamako ba.
Ku tuna cewa duk abin da mutum ya aikata, yana iya zama abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi gobe.
Allah Ya ba mu ikon kiyaye mutuncinmu, Ya tsare mu daga fitintinu na zahiri da na ɓoye, Ya kuma sa mu cikin bayinSa na gari.
Ilahee Ajeeb.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.
