Abba Anas Laushi: ‘Yan bindiga sun sako gawar jigon ADC bayan biyan fansar miliyan N50

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan garkuwa da mutane sun sako gawar tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma jigo a jam’iyyar ADC, Abba Anas Laushi bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa.

An sace marigayin ne tare da wani ɗan siyasa mai suna Ali Tukur Gantsa daga Jihar Jigawa a yayin da suke kan hanyar tafiya Abuja domin halartar babban taron ADC.

A cewar jaridar Daily Post, majiyoyi masu kusanci da iyalansa sun shaida cewa da fari ‘yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan 100 kana daga bisani aka cimma yarjejeniyar biyan miliyan N50, lamarin da ya yi sanadin sako Gantsa da kuma gawar Anas Laushi.

Wannan al’amari ya jefa mambobin ADC a Jihar Jigawa da abokan siyasarsu cikin jimami, inda da dama suka bayyana marigayin a matsayin mai sauƙin kai, manufa da ƙoƙarin hidima ga ƙasa.

Wata majiya ta ce, an yi awon-gaba da ‘yan siyasar biyu ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da suke kan hanyar tafiya daga Kano zuwa Abuja domin taron siyasa.

A cewarta, ‘yan bindigar sun tare su ne a yankin Jere da ke Jihar Kaduna, inda suka kutsa da su cikin daji ba tare da wani jinkiri ba.

Bincike ya nuna cewa, Anas Laushi na fama da cutar asma da hawan jini, wanda ya rasa magani a tsawon zamansa a hannun ‘yan garkuwar, lamarin da ya tsananta rashin lafiyarsa kuma ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

By Babaji