
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani malamin addinin Musulunci ya faɗa wa Babbar Kotun Tarayya cewa ya karɓi kuɗi domin yin addu’ar cimma nasara yayin shirin juyin mulki, amma ya yi gargaɗi ga masu shirin cewa akwai yiwuwar a yi rashin nasara.
Sheikh Sani Abdulƙadir, wanda shi ne na shida da ake tuhuma a shari’ar zargi kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya yi wannan iƙirari ne a wani faifan bidiyo da aka haska a kotun a ranar Litinin.
A faifan, Sheikh Abdulƙadir ya ce an same shi ne da batun ta hannun wani mai suna Sanda, domin ya yi addu’ar da ke goyon bayan shirin da aka zargi Kanal Maaji da jagoranta.
“Sanda ya faɗa min cewa ogansa ya yi nufin ƙaddamar da juyin mulki kuma yana buƙatar addu’a domin samun nasara a kai”, inji malamin. Bayan addu’ar, ya shaida wa masu bincike cewa ya shawarce su akan cewa akwai yiwuwar atisayen nasu zai yi rashin nasara kuma mutane biyu za,su tona asirin waɗanda ke da hannu a ciki.
Ya ƙara da cewa, daga bisani an sake neman sa da yin addu’a inda aka tura masa kuɗi a matsayin sadaka domin rufe bakin mutane biyun don kada su yi fallasa, waɗanda an tura sunayensu domin ƙarfafa hujja.
Daga bisani, Shehin ya ce ya gano kamen ne ta kafafen yaɗa labarai bayan Sanda ya shaida masa cewa tsawon kwanaki huɗu ana neman Maaji a waya ba a samun sa.
Haka kuma, malamin ya turje akan cewa kuɗaɗen na addu’a ne ba na taimaka wa juyin mulkin ba, yana mai cewa bai kai rahoton al’amarin ba ne saboda bai san wanda zai tunkara ba.
Daga nan ne Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 12 a Mayu, 2026 domin cigaba da sauraro.
