Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da nake wannan rubutu, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya amince da bayar da gudunmawar Naira Biliyan 2 da za a yi amfani da su wajen tallafawa waɗanda harin Anguwar Rukuba a Jos ya shafa, da ma rikicin da ya biyo baya. Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne, a yayin taron masu ruwa da tsaki da ya kira zuwa fadarsa, domin tattauna hanyoyin magance rikicin da ya addabi Jihar Filato tsawon shekaru. Shugaban ƙasa ya shaidawa shugabannin al’umma da suka je ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Caleb Mutfwang, waɗanda suka haɗa da tsofaffin gwamnoni, tsofaffin ministoci, da tsofaffin manyan jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, da malaman addini, cewa ba zai lamunci cigaba da asarar rayuka a dalilin addini da ƙabilanci, da siyasar ɗan ƙasa da baƙo ba. A saboda haka ya ba su shawarar su koma gida a fitar da rahotannin binciken da aka gudanar ƙarƙashin gwamnatocin baya, kan rikice-rikicen da aka yi, domin a duba a ga shawarwarin da za a iya aiki su, da hanyoyin da ya kamata a bi, don ganin an kawo ƙarshen waɗannan matsaloli.
Kodayake, ba yau ne aka fara irin wannan tattaunawa ba, an yi makamantan su da shugabannin ƙasa da suka gabata, amma muna da kyakkyawan fatan idan har aka yi abin da shugaban ƙasa ya ba da shawarar a yi, za a iya cimma nasara, da yardar Allah. Babban abin da zai ƙarfafa samun nasarar waɗannan shawarwari shi ne amincewar shugabannin siyasa da na al’umma, kan lallai suna son a zauna lafiya, kuma su yarda cewa ko wa ya saɓa wa dokokin ƙasa da matakin hukuma shi ma za a saɓa masa. A bai wa kowa dama da ƴanci daidai da kowanne ɗan ƙasa da ke zaune a Jihar Filato. A yi aiki da zuciya ɗaya, domin Allah, domin ganin cigaban al’ummar Filato bakiɗaya, ba tare da nuna wariya ba.
Matuƙar za a iya cimma haka to, babu shakka za a iya cewa an kama hanyar kawo ƙarshen rigingimun da suke addabar Jihar Filato. Amma matuƙar za a cigaba da zargin juna da ɗora laifin kan wani ɓangare, ko amfani da ƙarfin gwamnati ana cutar da wani sashi na al’umma, za a daɗe ba a cimma nasara ba. ɗaya daga cikin dalilan da ke kawo tarnaƙi a ƙoƙarin da ake yi na samar da ɗorewar zaman lafiya, shi ne rashin magana da zuciya ɗaya. A duk inda aka ce ana neman zaman lafiya, yarda da aminci to, wajibi ne a samu amana, gaskiya, da magana ɗaya, in kuwa aka rasa su za a cigaba da kwan-gaba-kwan-baya a wannan matsala.
Da fatan masu ruwa da tsaki a Jihar Filato za su haɗa kai su ajiye bambance-bambancen dake tsakanin su, su kalli cigaban jihar da al’ummarta, don Filato ta dawo da kwarjininta, ta samu ɗaukaka da ci gaban da take nema.
Idan mai karatu ya lura da taken rubutun wannan mako zai lura da yadda na danganta Jihar Filato da Jihar Neja, domin dukkansu jihohi ne da suke shiyyar tsakiyar Nijeriya, kuma suke fuskantar matsalolin tsaro. Sai dai ba kamar Filato ba, matsalar tsaron Jihar Neja ya fi nasaba da ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu aikata ta’addanci, da garkuwa da mutane musamman ’yan makaranta, da fararen hula, duk da kasancewar Jihar Filato ma tana fuskantar ire-iren waɗannan hare-haren ta’addancin.
A makon da ya gabata wata hidima ta ’yan uwa ta kai ni Jihar Neja, inda na bi hanyar Suleja daga Abuja, zuwa Minna, zuwa Kontagora har dai na dangana da ƙaramar Hukumar Rijau, daya daga cikin yankunan da ke iyaka da wasu ɓangarorin Jihar Neja dake fuskantar ƙalubalen ’yan bindiga. Duk da tsoro da fargaba da nake da shi game da halin da jihar ke ciki, amma shiga ta jihar na jinjinawa ƙoƙarin da gwamnati take yi, a matakin jiha da tarayya.
Duk wanda ya san yanayin hanyoyin Jihar Neja a baya, a yanzu zai yaba da gyare-gyare da ake yi, musamman a cikin garin Minna, da hanyar Kontagora har zuwa Rijau. Babu shakka shugabannin siyasa a jihar suna ƙoƙari sosai, saɓanin a baya yadda mutane ke fargabar bin hanyoyin jihar saboda lalacewa, kamar dai hanyoyin Adamawa da Taraba, da ake kuka da su.
A ɓangaren tsaro kuwa, nan ma gwamnati ta yi rawar gani, na ga yadda jami’an tsaro na soji ke ta sintiri akan manyan hanyoyin da ake yawan samun hare-haren ’yan ta’adda, duk da kasancewar babu wadatar jami’an tsaro a ƙasa, amma matakan da aka ɗauka a Jihar Neja ya taimaka sosai wajen samar da natsuwa a zukatan matafiya da sauran al’ummar jihar. Ya kuma rage karsashi da tasirin masu ta’addanci a ƙauyuka da birane.
Ina yabawa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Neja bisa hoɓɓasan da suke nunawa wajen ganin an yi maganin matsalar tsaro a jihar. Da fatan za a samu irin wannan sintiri na haɗin gwiwar jami’an tsaro a cikin garin Jos da manyan hanyoyin shiga cikin jihar, domin magance matsalar hare-hare kan matafiya da rikicin ƙabilanci da ke faruwa ba zato babu tsammani.
Sannan ina mai ba da shawara ga gwamnati ta ƙara ba da dama wajen ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da za su taimakawa waɗanda ake da su a ƙasa. Idan har shugabanni za su riƙa aiki da kalamansu, kuma za su cika alƙawuran da suka yi wa jama’a, ba sai a lokacin zaɓe ba, lallai za a samu sauyi mai girma a ƙasar nan.
