Mun rasa Saleh Shehu Ashaka!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun musamman ma samun kafafen sadarwa na yanar gizo ya zama kusan duk lokacin da mutum ya shiga yanar zai ga labarin rasuwar wani ko wata da batun shirya jana’iza. Hakanan akwai labarun rashin lafiya da wasu ma labarun masu sanya juyayi da zubar da hawaye.

Ranar Lahadi 3 ga watan nan na Oktoba 2026 da misalin ƙarfe 3 na rana sai wayata ta yi ƙara na ɗauka na duba sai na ga mai taimakawa shugaba Tinubu kan harkokin labaru ne Abdul’ziz Abdul’aziz. Da ya ke mun saba yin waya kan harkokin labaru bai ɗauka wani babban labari da zai girgiza ni har abada zai ba ni ba. Ya tambaye yi ko wane labari na ke da shi kan Saleh Shehu Ashaka. Nan na shaida ma sa na san ba shi da lafiya ya na kwance a asibiti a Masar. Nan ya fahimci ban san me ke faruwa ba, Allahu Akbar, nan ya shaida min Allah ya yi wa Saleh rasuwa! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Wallahi tun daga wancan lokaci har yanzu da na ke rubutun nan ban dawo cikin hayyacina ba don ƙirjina na cikin yanayi na nauyin juyayi kwatankwacin yadda na ji lokacin da mahaifina ya rasu. Nan dai labari ya ƙara fitowa wayata kuma ta ci gaba da kaɗawa daga masu neman sanin sahihancin labarin rashin. Haƙiƙa ina cikin manyan muƙarrabai na musamman in ma ba lamba daya ba na Saleh Shehu Ashaka. Na ɗau waya na fara bugawa mahaifin Saleh wato Alhaji Shehu Ashaka sai na fasa, Daga bisani na buga ma sa don gwada sanar da shi wannan labari na juyayi kuma cikin ikon Allah na ji cewa ashe ya samu labarin don ya ce mi ni “yaya haƙuri” wato don ya san yadda na ke kusa da dan nasa ya fara yi min ta’aziyya. Allah ya jiƙan Saleh da rahama. Ga yadda labarin rasuwa da bayani na gaggawa kan Saleh su ke:

Allah Ya Yiwa Shahararren ɗan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa

Allah ya yi wa ɗaya daga shahararrun wakilan kafafen labaru na duniya a Nijeriya Saleh Shehu Ashaka rasuwa bayan fama da jinya.

Saleh Ashaka wanda ya kara shahara a aikin jarida lokacin da ya yi aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka ɓoa a matsayin wakili daga Abuja, ya shafe shekaru ya na rubuce-rubuce kan yaƙi da cin hanci da rashawa da kafa gwamnatin adalci da a kan wallafa a jaridu ciki da Daily Trust.

Ashaka ya kasance cikin ‘yan jarida da wasu kafafe irin Aljazeera da CNN kan tuntuba kan muhimman labaru kuma ya na da tasiri a ayyukan da ya kan wallafa a dandalin ɗ da Instagram.

Saleh Ashaka ya yi hulɗa da manyan ‘yan jarida irinsu Aliyu Mustapha Sokoto na ɓoa, Ibrahim Alfa Ahmed, Christine Amanpour da sauransu.

A Abuja ya yi aiki tare da Nasiru Adamu El-hikaya, Madina Dauda, Umar Farouk Musa da sauran wakilai.

An haifi Saleh Ashaka a Jos jihar Filato a 1983 a cikin iyalin attajiri Alhaji Shehu Ashaka daga Kano da kuma mahaifiyarsa Hajiya Hauwa Tafisu daga jihar Adamawa.

Matashi, mai hazaka da mutunta jama’a, ya kai ziyara wajen mahaifiyarsa Hajiya Hauwa Tafisu da ta je jinya a Alkahira wato CAIRO na ƙasar Masar, inda a nan shi ma jinyarsa ta tashi inda ya cigaba da karɓar magani har ya kai ga matakin zafin ciwo na kimanin kwana 10 na zafin jiki, Allah ya karbi rayuwarsa.

‘Yan uwa da abokan aiki na cikin juyayi da taya juna ta’aziyyar rasuwar marigayin cikin yanayi na kaɗuwar zukata.

BA RABUWA DA GWANI BA… ALLAH YA JIƙAN SALEH SHEHU ASHAKA

Allah ya jiƙan shahararren ɗan jarida Saleh Shehu Ashaka da ya rasu a birnin Alkahira na Masar kuma a ranar Litinin 04/05/2025 da yardar Allah a ka gudanar da jana’iza a nan Alkahira “Cairo” bayan sallar azahar. Gabanin wannan jinya ta sa ta karshe, Saleh ya bugo min waya daga Doha cewa zai je Masar don duba Hajiya mahaifiyarsa da ta je can don duba lafiyarta. Allahu Akbar a Masar ɗin ne wannan jinya ta tashi ma sa shi ma a ka shiga duba shi har rai ya yi halinsa!.

Ina cikin juyayi ainun don yadda mu ke tare da shi zaman yaya da kani kuma a wani lokaci in aikin jarida ya yi zafi ko barci ma ba ya raba mu sai mun tabbatar mun yi abun da ya dace. Rahoton babban zaɓen Nijeriya na 2007, 2011, 2015 da 2019 duk mu na tare. Duk inda Saleh ya zaga a duniya ƙarshe ya kan so shiga Makkah don yin umrah. Ba shi da girman kai, ga karrama mutane cikin murmushi ga kuma zumunci. Kyautatawa jama’a kuma ya koya daga mahaifinsa Alhaji Shehu Ashaka wanda ke cikin manyan dattawa attajirai na Arewa na hannun daman marigayi Alhaji Aminu Dantata. Insha Allah zan faɗaɗa bayani kan rayuwar Saleh. Allah ya jiƙansa da rahama.

Gabanin marigayi Saleh ya rubuta takarda da hannunsa ya ajiye aikin ɓoa Hausa a wajajen shekara ta 2022 ya rika kawo min tunanin ajiye aikin don kama wasu ayyukan rayuwa na daban amma sai na riƙa buƙatar ya dakata tukun lokaci bai yi ba. Kasancewar yadda ya ke mutunta sai ya rubuta sanarwar ajiye aiki tsaf ya tura ba tare da na sani bay a kuma wallafa wasiƙar a shafinsa na yanar gizo. Hikimar Saleh ita ce ya yanke matsaya ajiye aikin kuma ba ya son irina da ya ke kawaicin ƙin bin shawararsu su sani don dakatar da shi. A cikin wasiƙar nan ya rubuta shaidar rayuwar amana da mu ka yi da shi don wasu su kan ganmu tare amma ba su san a gida ɗaya mu ke da zama ba.

Kasancewar ƙarancin mutane da su ka samu tafiya can Masar don shaida jana’izar Saleh, abokan aiki da sauran muƙarrabai mun halarci sallar jana’izar salatul ga’ib ga marigayin da a ka gudanar a babban masallacin ƙasa da ke Abuja. Taron wannan sallar ya kara zama wata dama ta taruwar jama’a da ya zama bigiren miƙa ta’aziyya. Manyan ‘yan jarida irin tsohon shugaban sashen Hausa na BBC Mansur Liman, Isah Sunsu na AMNESTY, Jafar Jafar na Daily Nigerian, Aliyu Tanko na BBC, Buhari Fagge na BBC, Uwais Abubakar Idris na DW da tsohon daraktan labaru na hukumar alhazai NAHCON Alhaji Uba Mana na daga waɗanda su ka samu halartar jana’izar. Mata ma sun samu halartar jana’izar irinsu Zainab Buba Galadima da Hajiya Zainab Bununu da sauransu. Hakanan akwai sauran muƙarrabai irin Mahmud Ribadu, Shitu Muhammad Kabir =, Dokta Hamza Alhassan Sa’id, Mustapha Alhassan na hukuamr tashar jiragen ruwa, Awwal Musa Bashir, Umar Muhammad Gombe na Kaftan tɓ da sauransu.

Haƙiƙa duk waɗanda su ka halarci wannan jana’iza na furta labarun ayyukan alheri da Saleh ya aikata garesu ko wasu da su ka sani. Kyakkyawar shaida da marigayi ya samu ta zama abun buƙata ga duk mai neman rahama ya zama bayan rayuwarsa a rika furta ayyukansa na alheri. A shekarun baya marigayin kan nuna min kayan sawarsa sai ya ce duk na rabarwa jama’a bayan ya rasu! Duk tunaninsa mutane su amfana da shi ko da bayan ba ya raye. Ba zan manta ba hatta a wannan jinya ta sat a karshe duk lokacin da mu ke waya ya kan ce shi dai a gaskiya kamar ya kammala dukkan abubuwan da ya ke son gudanarwa a duniya kuma ko yanzu ya koma ga Allah ya na ƙara addu’ar samun rahama ba komai. Haƙiƙa bai ɗauka bankwana ce ta wata siga ya ke yi min ba don haƙiƙa har jiki Saleh kan yi in ya samu sauki kuma ya rika ziyartar jama’a don sada zumunci.

Ga wanda ya ke ganin Saleh daga nesa ba mamaki zai ɗauka mutumne mai son shagali a rayuwa wajen son zagawa biranen duniya da yawo a jiragen sama. Haƙiƙa wasu tafiye-tafiyen da ya ke ma duk zuwa duba lafiyarsa ne a asibitoci a ketare amma ba ya nuna ya na fama da jinya ga ‘yan gajerun bidiyo da ya kan fitar ko rubuta wasu kalamai masu sanya kwarin guiwa da shawarwari na rayuwa mai ma’ana. Kazalika Saleh kan so ya rayu cikin talakawa kuma zai iya zama a wajen da ma ba ababen more rayuwa sam don more rayuwa ba ɗabi’arsa ba ce sam. Duk da marigayin ya na da hanyar samun dukiya da yin ratuwa ta kasaita amma hakan sam ba hanyarsa ba ce don ya fi son rayuwa a tsakiyar mutanen da ke da ƙaramin ƙarfi.

KAMMALAWA

A ƙarshen rayuwarsa, Saleh ya yi ta yi wa mutanen da ya sani alheri kama da na kuɗi, kayan abinci da sauran duk abubuwa na tallafin rayuwa. Ya na kwance a asibiti amma wasu da ba su sani ba, na bugo ma sa waya don ya tallafa musu da kuɗin sayen abinci ko magani, kuma nan take ya kan tallafa da ninkin-ba-ninkin buƙatar da a ka gabatar ma sa. Saleh a ‘yan shekarunsa na matashi har ya koma ga Allah bai bar wani abokin faɗa ko adawa ba. Ya taɓa shaida min cewa shi ya ma daina muhawara da za ta kawo taɓa zuciyar wani don muradin ya zama kullum a na zaune lafiya ta mutunta ra’ayoyin jama’a.

By ukarofi