An fara raba magunguna a asibitocin Bindawa da gwamnatin Katsina ta samar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Shugaban ƙaramar hukumar Bindawa, Hon. Badaru Musa Giremawa, ya ƙaddamar da rabon magungunan da gwamnatin jihar ta samar domin asibitocin ƙaramar hukumar Bindawa, a wani mataki na inganta harkokin kiwon lafiya da tabbatar da samun ingantattun magunguna ga al’umma.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Abubakar Hamisu Doro wanda ya fitar da sanarwa ya ce shugaban,ya hori malaman kiwon lafiya da su guji karkatar da magungunan da kawo domin al’ummar inda yayi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu wajen satar magungunan to ya kuka da kansa.

Gwamnatin katsina ta samar tare da rarraba magungunan da ƙananan hukumomin da ke jihar domin kyautata kiwon lafiya.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Hon. Badaru Musa Giremawa ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa ɓangaren lafiya da sauran fannoni na ci gaban al’umma a faɗin jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar ya jagoranci taron majalisar tsaro (Security Meeting) na ƙaramar hukumar, wanda ya haɗa shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki. Taron ya tattauna kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙaramar hukumar tare da samar da dabarun magance matsalolin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Giremawa ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply