Daga USMAN KAROFI
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa har yanzu akwai babban haɗarin shigowar nau’in cutar Ebola na Bundibugyo zuwa Najeriya, sakamakon ci gaba da yaɗuwar cutar a wasu ƙasashen Gabashin Afirka, yawaitar zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe da kuma iyakokin da ba su da cikakken tsaro.
Darakta janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Legas, inda ya ce hukumar ta gudanar da wani nazari na musamman domin tantance haɗarin da Najeriya ke fuskanta. Ya ce duk da cewa ba a samu wani tabbataccen mutum da ya kamu da Ebola a Najeriya ba, hukumar na ɗaukar matakan kariya da sa ido domin hana shigowar cutar cikin ƙasar.
Dakta Idris ya bayyana cewa alamomin Ebola suna kama da na wasu cututtuka da ake yawan samu a Najeriya kamar zazzabin cizon sauro da zazzabin Lassa, lamarin da ka iya jinkirta gano masu ɗauke da cutar. Saboda haka ya buƙaci ma’aikatan lafiya a dukkan matakai su kasance cikin shiri tare da kula da duk wata alama da ka iya nuna kamuwar mutum da Ebola.
Ya ce NCDC ta riga ta ƙarfafa sa ido a filayen jiragen sama da sauran wuraren shiga na ƙasa, tare da inganta shirye-shiryen ɗakunan gwaje-gwaje, wayar da kan jama’a, kula da masu fama da cututtuka da kuma haɗin gwiwa da hukumomin lafiya na jihohi da na ƙasa. Haka kuma ya buƙaci gwamnatocin jihohi su tabbatar da cewa cibiyoyin gaggawa da tsarin daƙile annoba suna aiki yadda ya kamata.
Hukumar ta sake jaddada aniyarta ta yin aiki tare da gwamnatocin jihohi, cibiyoyin lafiya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin ƙarfafa shirin kariya da martani ga cututtuka masu yaɗuwa.
A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), ɓarkewar Ebola da ake fama da ita a halin yanzu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta haddasa ɗaruruwan masu kamuwa da cutar da kuma mutuwar mutane da dama, lamarin da ya sa Najeriya ke ɗaukar matakan kariya cikin gaggawa.
