Daga NASIR S. GWANGWAZO
Daga dukkan alamu Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki matsaya kan wanda zai tsaya wa Jam’iyyar APC takarar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ɓagwai da Shanono a babban zaɓen 2026, inda yake ƙoƙarin mika takarar ga wanda ba shine akasarin al’ummar yankin suke so ba, duk da cewa, mazaɓar tana da mai neman takarar wanda duk Nijeriya an yarda da tasirinsa a majlisar dokoki ta ƙasa, wato tsohon ɗan majalisa, Hon. Farouk Lawan.
Sunan Hon. Farouk Lawan ba baƙon abu ba ne a siyasar Nijeriya, ballantana ta Jihar Kano, mahaifarsa, saboda tasirin da ya yi a majlisar wakilai lokutan gwamnatoci daban-daban da suka shuɗe kama daga ta Obasanjo, Yar’Adua zuwa ta Jonathan, inda har aka rika yi masa lakabi da ‘Mr. Integrity’ ko ‘Ka fi sipika’.
A lokacin da Farouk Lawan ke sharafinsa a majalisar dokoki ta tarayyar Nijeriya, kowa ya yarda cewa, majalisar tana da nagarta fiye da yadda ake gani bayan da ba ya nan daga zamanin gwamnatin Buhari zuwa yanzu, saboda yadda a lokutansa majalisar wakilai ke iya taka wa ɓangaren zartarwa birki a duk lokacin da aka nemi kauce hanya.
Amma sai dai hakan ba ya nufin a lokacin da Faruku ke majalisa, ita majalisar ba ta mara wa ɓangaren zartarwa baya kan kyawawan manufofin da suka zo da su a ko yaushe, illa dai kawai ana yin abun ne cikin mutuntaka da bin doka da ƙa’idojin aiki. Babban misali shine, yadda aka zauna lafiya tsakanin majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa a zamanin Marigayi Yar’Adua, gwamnatin da ake kallo a matsayin mafi nagarta da aka taɓa yi tun bayan kafa wannan Jamhuriya ta huɗu.
Wannan tsari na daga cikin dalilan da suka sanya Shugaba Tinubu ya yi yafiya ga Hon. Farouk Lawan bayan da ake ganin gwamnatin Jonathan ta shafa masa kashin kaji, sannan gwamnatin Buhari ta kasa yi masa abin da gwamnatin Tinubu ta yi na yafiya. Yafe wa Hon. Farouk Lawan na ɗaya daga cikin abubuwan da Tinubu ya yi wa ’yan Arewa, waɗanda ba za a taba mantawa da su ba, saboda Shugaba Tinubu yana da basirar gane cewa, samun irin su Faruku a majalisar dokoki zai taimaka matuƙa gaya wajen dawo da martabar Nijeriya a idanun duniya ba tare da kace-nace tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa ba. Bai dace Gwamnan Kano ya hana wa Nijeriya samuwar hakan ba.
A yanzu da ake ganin al’amura sun cakuɗe kan yadda ake tafiyar da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, manazarta da dama suna kallon hakan yana da nasaba da yadda Majalisar Dokoki ke tafiyar da dangantakarta da ɓangaren zartarwa, inda wasu ke ganin cewa, majalisar ta ƙasa ba ta taimaka wa ɓangaren zartarwa wajen aiwatar da kyawawan manufofin da Gwamnatin Tinubu ta tsara har ma ake kallon ta a matsayin gwamnatin da ta yi baƙin jini a idanun ’yan ƙasa, alhali wasu manufofin da ta ke gabatarwa za a ga amfaninsu a nan gaba, amma yadda ake gabatar da su a majalisa kuma ake amincewa da su kai tsaye ne yake janyo surutai a tsakanin ’yan Nijeriya, musamman ’yan Arewa.
Wannan ya sanya ake kallon majalisa a matsayin ’yar amshin Shata.
Don haka lallai ya dace a samu ƙwararru a Majlisar Dokoki ta ƙasa, waɗanda za su iya amfani gogewarsu wajen ganin an saisaita al’amura, kamar yadda ya faru a lokacin Yar’Adua, domin ba ko yaushe ba ne faɗa da ɓangaren zartarwa ke amfanar ’yan kasa.
Daƙile dawowar Farouk Lawan zuwa majalisa a wannan lokaci zai kawo cikas ga manufofin Tinubu na ganin an dawo da martabar Gwamnatin Tarayya da ita kanta majalisar, kuma koma-baya ne ga jihar Kano da Arewa, domin akwai buƙatar samun gogaggu, waɗanda ba dolaye ba ne, a majalisar dokoi kuma ɗan majalisa ɗaya tamkar da goma irin Faruku, don saita al’amura.
Haƙiƙa lallai ya wajaba ga Gwamna Abba Yusuf ya fahimci Shugaba Tinubu akan batun nan na tsayar da ɗan takara kuma ya gane alƙiblar al’ummar mazaɓar Ɓagwai da Shanono da Jihar Kano da Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya!
Rigingimun da ake haifarwa da sunan masalaha a wajen tsayar da ’yan takarar APC, tabbas wagegiyar ƙofa yake buɗewa ga ’yan adawa, waɗanda a shirye suke su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin jihar!
Nasir Gwangwazo ɗan jarida ne mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya.
