Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sojoji na 17 Brigade sun kashe “yan bindiga tare tare da makamai a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.
A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar Abayomi Adisa ya ce sojojin waɗanda ke da sansani a jami’ar FUDMA sun sanya shind a hanyar Turare zuwa Kitibawa zuwa Kuka da .
Ya bayyana cewa ‘yan bindigan da ke da sansani a wuraren Matazu sun shiga tarkwon sojojin 17 Brigade inda sojojin suka sami galaba bayan an samu tsawon lokaci ana fafatawa a tsakanin su.
Mr Abayomi ya ce sojojin sun sami nasarar kashe mutane 3 da gano bindiga kirar AK 47 da harsashi Da dama, sai babur na hawa guda ɗaya da kuɗi Naira 3,500 da ‘yan bindigan.
Sojojin sun kira ga al’ummar jihar da taimakawa sojoji da bayanan sirri da zai taimaka wajen gano ‘yan ta’adda da sauran miyagun mutane a faɗin jihar.
