Nasarawa 2027: Dakta Zakka ya sanar da niyyar takarar gwamna a hukumance

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Tsohon Akanta Janar kuma Sakatare na dindin na Ofishin Liaison, Abuja, Dr. Zakka Yakubu ya sanar a hukumance niyyar sa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a babban zaɓen 2027 a inuwar jami’ar APC mai ci a jihar.

Da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayansa daga ƙananan hukumomi 13 na jihar waɗanda suka yi cinci-rindo a wajen wani babban taro da aka gudanar a makarantar firamare ta tsakiya a Akwanga a ƙarshen makon da ya gabata Dr. Zakka ya ce ya yanke shawarar gabatar da kansa ne domin yi wa mutanen jihar Nasarawa hidima ta wata sabuwar hanya bayan ya yi shawarwari da dukkan ƙungiyoyi masu ruwa da tsaki a jihar ciki har da dattawa da shugabannin al’umma da kwararru da ƙungiyoyin matasa da abokai a faɗin jihar gaba-ɗaya.

Dr. Zakka Yakubu wanda aka san shi da ayyukan agaji da tausayin talakawa ya ce ƙwarewar da ya tara tsawon kusan shekaru talatin a lokacin da ya yi aiki da cibiyoyin gwamnati daban-daban da abokansa da ma’aikatan gwamnati a matakai daban-daban ya sa ba shi da shakka cewa ya cancanta ya jagoranci mutanen jihar Nasarawa wajen amfani da dimbin tattalin arziki da ke jihar domin amfanin kowa da kowa.

Ya cigaba da bayyana cewa “Rayuwata a harkar gwamnati ta koya mini mahimmancin ladabi da kula da kuɗi da gaskiya da jagoranci mai alhakin. Ban shigo siyasa don neman riba ta kaina ba na fito ne domin ina ganin jihar Nasarawa ta cancanci shugabanci mai gaskiya da ƙwarewa da kuma mai mayar da hankali kan kawo sakamako ga talakawa.

“Ina ganin za a iya sauya jihar mu idan muka yi amfani da sarrafa albarkatu cikin hikima da tsare-tsaren cigaba masu jarumtaka amma masu alhaki da siyasa mai ɗaukar kowa a ciki wadda ba za ta bar wata al’umma a baya ba.”

Ɗan takar gwamnan ya kuma lura cewa jihar Nasarawa tana da mutane masu ilimi sosai da masu himma da juriya da kuma ƙasa dake da matuƙar arziki a fannin noma da ma’adanai amma ya ce mutanen jihar dole su ƙara ƙoƙari wajen mayar da waɗannan albarkatu zuwa damammaki ga ‘yan ƙasa.

“Dole ne mu gina tattalin arziki da zai samar da ayyukan yi wa matasanmu. Dole ne mu ƙarfafa ilimi da lafiya. Dole ne mu tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a,” in ji Dr. Zakka.

Ya yi alƙawuran da dama idan ya zama gwamnan jihar Nasarawa da yardar Allah waɗanda suka haɗa da saka hannun jari a ilimi da horar da ƙwarewa don shirya matasa ga ayyukan yau da gobe da ƙarfafa fannin Ilimi tare da mayar da hankali kan lafiyar uwa da yara da kuma tallafa wa mata da samun jari da horo domin su zama ginshikin cigaban iyali da al’umma.

Haka kuma, a sakonnin fatan alheri daban-daban shugabannin kwamitocin yaƙin neman zaɓen Dr. Zakka daga dukkan ƙananan hukumomin jihar sun yaba wa ɗan takarar musamman saboda ayyukan agaji da ya ke yi tsawon shekaru da dama inda suka ce yanzu ne lokacin da mutanen jihar za su saka masa ta zabin shi a matsayin lamba daya a jihar.

Sun kuma yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin tabbatar da nasararsa a zaɓen fidda gwani na APC mai zuwa da kuma babban zaɓe.

By ukarofi