Gina jami’o’i biyu a Kano ne ya sa muke son Kwankwaso — Hon. Sa’ad Darki

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu yabo daga Hon. Sa’ad Ibrahim Darki, wanda aka fi sani da Janar, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa ilimi a jihar Kano.

Hon. Sa’ad Janar ya bayyana cewa gina jami’ar Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUSTECH) Wudil a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003, da kuma jami’ar Northwest University a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu daga 2011 zuwa 2015, na daga cikin manyan dalilan da suka sa yake goyon bayan Kwankwaso.

Ya ce Kwankwaso ya nuna kishin ilimi musamman ga ‘ya’yan talakawa, matasa da mata, ta hanyar samar da cibiyoyin koyon sana’o’i guda 24 da kuma makarantun SAS da Technical a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

A cewarsa, irin wadannan ayyuka sun nuna kishin al’umma da hangen nesa wajen bunkasa rayuwar jama’a.

Hon. Sa’ad Janar ya kara da cewa a matsayinsa na dan siyasa, yana bin tafarkin Kwankwaso ne saboda irin manufofinsa na ci gaban al’umma da kishin kasa.

Ya bayyana cewa duk inda Kwankwaso yake a siyasance, a nan ne matsayinsa yake, yana mai jaddada cewa ya dade yana gwagwarmayar siyasa tun yana matashi har zuwa yanzu.

By ukarofi