Kano: Masu kishin ilimi sun tallafa wa makarantar Subulus Salam a Darki

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Mutane da dama masu kishin ilimi da harkar addini sun bayar da tallafi ga makarantar Madarasatul Subulus Salam Lit Tahfizul ƙur’an da ke Masjidul Jami’u Ummi Fahad, Sabuwar Unguwa Darki, a ƙaramar Hukumar Wudil ta jihar Kano.

An gudanar da taron ne a yayin bikin yaye ɗalibai 28 da suka haddace Alkur’ani mai girma, ciki har da wani ɗalibi mai shekara 12 kacal, kamar yadda shugaban makarantar, Malam Bello Ridwan, ya bayyana.

Daga cikin waɗanda suka bayar da tallafi akwai Injiniya Lawan Musa Mustapha, shugaban kamfanin Lafiz Engineering and Construction Nigeria Limited, wanda ya bayar da gudummawar naira dubu 250 domin tallafa wa makarantar.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na ɗan asalin Darki, yana alfahari da irin ci gaban da makarantar ke samu, tare da kira ga gwamnati da al’umma da su ƙara bai wa ilimi da tarbiyya muhimmanci domin samar da ingantacciyar rayuwa a cikin al’umma.

Haka zalika, Injiniya Lawan Gambo Datti ya bayar da tallafin naira dubu 100, sannan ya yi alkawarin bayar da gudummawar kwarewarsa wajen kula da aikin ginin makarantar idan aka fara aikin.

Shi ma Kansilan mazaɓar Darki, Hon. Kawo Saleh Darki, ya raba kayan sawa ga daliban makarantar, inda ya bai wa dalibai mata atamfa guda 15, yayin da dalibai maza suka samu yadi guda uku-uku a matsayin kyauta.

Kansilan, wanda ya wakilci dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Wudil, Hon. Ali Manaja, ya ce dan majalisar na farin ciki da irin nasarorin da makarantar ke samu, yana kuma ci gaba da kokarin bunkasa harkar ilimi a yankin.

A nasa ɓangaren, wakilin kwamishinan filaye na jihar Kano, Kawo Dattijo, ya bayyana cewa da zarar an samar da fili domin gina makarantar, ma’aikatar filaye karkashin jagorancin Hon. Umar Abduljabbar Garko za ta bayar da cikakken hadin kai domin tabbatar da aikin ya tabbata.

Ya kuma bayar da gudummawar naira dubu 100 a madadin kwamishinan.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Hon. Sa’ada Ibrahim Darki, wanda aka fi sani da Janar, tare da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Kano.

By ukarofi