Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi kamfanonin sadarwa kan matsalar sabis

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙara matsa lamba kan kamfanonin sadarwa domin inganta ayyukansu a faɗin ƙasar, tana mai jaddada cewa lokaci ya yi da masu amfani da layukan waya za su fara jin daɗin ingantacciyar sadarwa da kuma samun ƙimar kuɗin da suke kashewa.

Ministan Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Fasahar Zamani, Bosun Tijani, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, inda ya ce gwamnati ta riga ta aiwatar da manyan sauye-sauye domin farfaɗo da ɓangaren sadarwa.

Ya ce yanzu ya rage wa kamfanonin sadarwa su magance matsalolin rashin ingantacciyar sabis da ke addabar miliyoyin masu amfani da layukan waya a ƙasar.

“Yanzu alhakin kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Globacom da T2 ne su ɗauki matakan da suka dace domin warware matsalolin sabis tare da samar da irin sabis ɗin da ’yan Nijeriya suke buƙata,” inji Tijani.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin yanzu ta gaji matsaloli masu ɗorewa a ɓangaren sadarwa, waɗanda suka samo asali daga rashin wadataccen zuba jari a muhimman kayayyakin more rayuwa tsawon shekaru.

A cewarsa, matsalolin rashin sabis da katsewar sadarwa suna da alaƙa da ƙarancin kayan aiki da suka hana kamfanonin sadarwa samar da ingantaccen sabis a duk faɗin ƙasar.

Domin magance matsalar, Tijani ya ce gwamnati ta ɗauki matakai na gaggawa da kuma na dogon lokaci domin sauya fasalin kayayyakin sadarwar dijital a Nijeriya.

Dangane da shirin na dogon lokaci, ya bayyana cewa gwamnati ta samu tallafin kuɗi ƙarƙashin jagorancin Bankin Duniya tare da samar da wani tsari ta hanyar Project BRIDGE domin faɗaɗa layukan fibre-optic a faɗin ƙasar.

“Mun samu tallafin kuɗi daga Bankin Duniya tare da kafa tsarin musamman a ƙarƙashin Project BRIDGE domin samar da ingantaccen tsarin fibre-optic da kowa zai iya amfani da shi a faɗin ƙasa,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa kafin ƙarshen shekarar nan za a fara shimfiɗa layukan fibre da kuma kafa ƙarin hasumiyoyin sadarwa ta hanyar NUCAP, tare da ƙoƙarin faɗaɗa ƙarfin sadarwar tauraron ɗan adam.

Tijani ya ce ana sa ran waɗannan zuba jari za su rage giɓin kayayyakin sadarwa cikin shekaru biyu zuwa biyar masu zuwa tare da inganta samun intanet da kwanciyar hankali a harkokin sabis a Nijeriya.

Da yake bayyana manufar gwamnati, ministan ya ce ana son tabbatar da cewa ’yan Nijeriya suna samun intanet mai sauri kuma mai inganci kai tsaye a gidajensu da wuraren kasuwanci.

“Ya kamata ƙaramin ɗan kasuwa ya iya samun fibre internet mai sauri da inganci kai tsaye a gidansa ko shagonsa, maimakon dogaro da na’urorin dongle ko network mara tabbas,” inji shi.

Ministan ya kuma bayyana wasu sauye-sauyen gaggawa da gwamnati ta aiwatar domin ƙarfafa ɓangaren sadarwa, ciki har da daidaita kuɗin haraji, ayyana kayayyakin sadarwa a matsayin muhimman kayayyakin more rayuwa na ƙasa, da sauran sauye-sauyen tattalin arziki.

A cewarsa, waɗannan matakai sun samar wa kamfanonin sadarwa yanayi mafi inganci da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu, har ma wasu daga cikinsu suka koma samun riba.

“Yanzu suna aiki a cikin yanayi mafi kwanciyar hankali, mai gaskiya kuma mai tafiya da tsarin kasuwa, kuma sun koma samun riba,” inji Tijani.

Ya ƙara da cewa, yanzu kamfanonin sadarwa suna da ƙarfin kuɗi da kuma yanayin gudanarwa da zai ba su damar inganta ayyukansu.

Ministan ya bayyana cewa an bai wa NCC cikakken iko domin sa ido kan ayyukan kamfanonin sadarwa, tabbatar da bin ƙa’idoji da kuma hukunta waɗanda suka gaza idan buƙatar hakan ta taso.

Ya ce, gwamnati za ta riƙa amfani da rahotannin hukumar da kuma koke-koken masu amfani da layukan waya domin riƙe kamfanonin sadarwa da alhakin ayyukansu a watanni masu zuwa.

Tijani ya nuna fata cewa nan gaba kaɗan ’yan Nijeriya za su fara ganin sauye-sauye masu ma’ana a ingancin kira, ayyukan data da kuma faɗaɗa sabis a faɗin ƙasa.

By ukarofi