Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa rasuwar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ce ta jawo rikice-rikicen da ake samu kan tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu a Nijeriya.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ, inda ya kare matakin da jam’iyyar NDC ta ɗauka na bai wa yankin Kudu tikitin shugaban ƙasa domin zaɓen 2027.
A cewarsa, bai wa Kudu damar ci gaba da mulki shi ne mafita mafi dacewa domin kawo ƙarshen cece-kuce kan tsarin zoning da rabon mulki.
“Mun yi imanin cewa mafita mafi kyau yanzu ita ce a bai wa Kudu mulki domin kawo ƙarshen rikicin da ya samo asali bayan rasuwar ɗan’uwanmu Umaru Musa Yar’adua. Wannan ne ya jefa tsarin cikin ruɗani,” inji Kwankwaso.
Ya bayyana cewa bayan rasuwar Yar’adua a shekarar 2010, mataimakinsa Goodluck Jonathan daga Kudu ne ya karɓi mulki, sannan ya sake lashe zaɓe a 2011, lamarin da ya ƙara haddasa muhawara kan rabon mulki.
Kwankwaso ya ce har yanzu ana samun saɓani kan yadda ake lissafin shekarun da Arewa da Kudu suka yi suna mulki, inda kowane ɓangare ke kallon batun ta yadda zai amfane shi.
Sai dai ya bayyana cewa jam’iyyar NDC ta yanke shawarar fara lissafin daga ƙarshen mulkin Muhammadu Buhari, wanda ya yi shekaru takwas a mulki.
“A yanzu idan aka fara daga Buhari, za a ce Kudu na kan wa’adinta na farko ne kawai, wanda zai cika shekaru huɗu nan da shekara guda,” ya ce.
Kwankwaso ya ƙara da cewa shugabannin siyasa daga Arewa da suka shiga jam’iyyar NDC sun amince da tsarin ba tare da gardama ba saboda muhimmancin haɗin kai a cikin jam’iyyar.
Sai dai ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci ga Nijeriya ba wai shugaban ƙasa daga Arewa ko Kudu ba ne, illa samun shugabanci nagari.
“A yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne samun shugabanni masu ƙwazo, jajircewa da kishin ci gaban ƙasa,” inji shi.
Kwankwaso da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi sun shiga jam’iyyar NDC ne a ranar 3 ga watan Mayu bayan ficewarsu daga jam’iyyar ADC sakamakon rikice-rikicen cikin gida.
A babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, NDC ta tabbatar da bai wa yankin Kudu tikitin shugaban ƙasa na 2027.
