Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargadin cewa bai wa ɗan takara daga Kudancin Nijeriya tikitin shugaban ƙasa a tsakanin jam’iyyun adawa a zaɓen 2027 zai iya raunana ƙoƙarin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olusola Sanni, ya fitar, inda ya bayyana kiran a bai wa Kudu tikitin shugaban ƙasa a matsayin abu da “zai cutar da jam’iyyun adawa.”
Ya tambaya cewa ta yaya ɗan takarar adawa daga Kudu zai iya kayar da shugaban ƙasa mai ci wanda shi ma daga Kudu yake.
A cewarsa, nasarar zaɓe tana buƙatar dabarun siyasa da fahimtar yanayin ƙasa, ba wai dogaro da ra’ayin yanki kawai ba.
Atiku ya kuma yi nuni da cewa a tarihin Nijeriya babu wani shugaban ƙasa mai ci da aka taɓa kayarwa da ɗan takara daga yankinsa.
Ya ƙara da cewa zuwa shekarar 2027, yankin Kudu zai shafe kusan shekaru 18 yana mulki a jamhuriya ta huɗu, yayin da Arewa ta yi kusan shekaru 10 kacal.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi wasu masu goyon bayan tsarin rabon mulki da nuna son kai, yana mai cewa da dama daga cikinsu sun goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan bayan rasuwar Umaru Musa Yar’adua a 2011.
Dangane da batun bai wa yankin Kudu maso Gabas damar shugabanci, Atiku ya ce yankin na buƙatar sahihiyar hanya mai ɗorewa ta kaiwa ga shugabancin ƙasa, ba wai abin da ya kira “alamar nuna tausayi kawai ba.”
Kalaman Atiku na zuwa ne yayin da jam’iyyun adawa ke ci gaba da tattaunawa kan batun haɗaka da kuma yadda za su tsara tikitin shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
