Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa a shirye yake ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa daga Kudancin Nijeriya idan jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta yanke hakan gabanin zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin PrimeTime na gidan talabijin na Arise Tɓ, inda ya ce jam’iyyar ta amince da bai wa Kudancin Nijeriya tikitin shugaban kasa na wa’adi guda domin tabbatar da daidaito da hadin kai a kasa.
Ya ce, “Idan jam’iyya ta yanke shawarar in zama mataimakin wani dan takara daga Kudu, a shirye nake.”
Kwankwaso, wanda ya hada kai da tsohon dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, a karkashin NDC, ya bayyana cewa sun cimma matsayar ne bayan tuntuba da shugabanni da masu ruwa da tsaki daga sassan kasar nan.
Ya ƙara da cewa babban abin da Nijeriya ke bukata yanzu shi ne shugabanci nagari mai kishin ƙasa, ba wai batun Arewa ko Kudu kadai ba.
A cewarsa, shi da Peter Obi sun tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro musamman a Arewacin Nijeriya, yana mai bayyana cewa suna da kwarewar da za ta taimaka wajen kawo sauyi a kasar.
Kwankwaso ya kuma nuna yiwuwar sake hada kai da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, duk da bambancin siyasa da ke tsakaninsu a baya.
Ya ce matasa ne za su taka muhimmiyar rawa a zaben 2027, yana mai bayyana cewa motsin Kwankwasiyya da na Obidient suna da akida iri daya ta sauyi da cigaba.
Haka kuma ya soki wasu gwamnoni a kasar nan, yana zargin cewa da dama daga cikinsu sun dogara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin samun nasara a zaben 2027.
Kwankwaso ya ce yanzu al’ummar Arewa sun fara canza tunani, inda ya bayyana cewa mutane ba sa son siyasar rabon kayan abinci kawai, illa suna bukatar shugabanci mai nagarta da kawo cigaba.
