Rahoto

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da kalmar ‘Dakta’

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da kalmar ‘Dakta’

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabuwar doka wadda ta hana duk wanda aka ba wa digirin girmamawa, wato ‘Honorary Doctorine Degree’, amfani da laƙabin “Dakta” a farkon sunansa a kowane fanni na hukuma, ilimi ko sana’a, tana mai cewa hakan na nuni da yaudara da karkatar da gaskiyar cancantar ilimi. Ministan Ilimi, Malam Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja yayin ganawa da ’yan jarida, inda ya ce an amince da sabuwar manufar ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) domin daidaita tsarin bayar da digirin girmamawa a…
Read More
Farfesa Abdallah Uba Adamu: Shekaru 70 na ilmi, bincike da sauya tarihi

Farfesa Abdallah Uba Adamu: Shekaru 70 na ilmi, bincike da sauya tarihi

Daga IBRAHIM HAMISU A ranar 25 ga Afrilu, 2026, al’ummar ilimi a Nijeriya, musamman na Jami’ar Bayero da ke Kano, sun yi wa wani babban gwarzon ilimi bankwana na kammala aiki bayan sama da shekaru 40 yana koyarwa, bincike da jagoranci. Ritayar Farfesa Abdallah Uba Adamu ba kawai ƙarshen aikin gwamnati ba ne, a'a wata muhimmiyar alama ce ta cika tafiyar rayuwa mai cike da hidima ga ilimi, al’adu da cigaban al’umma. A tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama ɗaya daga cikin fitattun malaman jami’a da suka haɗa ilimin kimiyya da na zamantakewa…
Read More
Aure babu bincike: Son rai ko ganganci?

Aure babu bincike: Son rai ko ganganci?

Daga AISHA ASAS  Annabin Rahma (S.A.W) ya ce, "Idan ku ka samu wanda ku ka yarda da halinshi, to ku ba shi aure........." Ta yaya iyaye za ku iya gane halin mutum idan ba ku yi bincike ba? Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Fatan Allah ya sa mu amfana da juna. Bincike wani muhimmin abu ne ko ince ɗaya ne daga cikin tubali da ake gina aure kansa, kuma za mu iya amincewa da cewa, dukka malamai sun yi ijtima'i akan yin sa shi ne mafi a'ala akan…
Read More
Matsalar fanshon ’yan sanda: Buƙatar gaggawar gyara don kare martabar masu ritaya

Matsalar fanshon ’yan sanda: Buƙatar gaggawar gyara don kare martabar masu ritaya

Zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Masu Ruwa da Tsari, Assalamu alaikum. Wannan wasiƙa na zuwa ne cikin girmamawa da kuma nuna damuwa mai zurfi dangane da halin ƙunci da wahala da tsoffin jami’an ’yan sandan Nijeriya ke fuskanta bayan sun kammala hidimarsu ga ƙasa. Lamarin ya zama abin takaici matuƙa, har ya kai ga haifar da zanga-zanga, koke-koke da kuma kiraye-kirayen neman gyara daga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare doka da oda a cikin al’umma. Ba sabon abu ba ne cewa batun fansho na ’yan sanda ya daɗe yana jan hankali a ƙasar nan. Tun bayan ƙaddamar…
Read More
Nakasa a mahangar karin magana: Guzurin Ranar Nakasassu ta Duniya 

Nakasa a mahangar karin magana: Guzurin Ranar Nakasassu ta Duniya 

Daga MUJAHEED ABDULLAHI KUDAN Shimfiɗa tabarma: Nakasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana, (CNHN, 2006: 356). Saboda haka, nazarin nakasa fage ne da ke ƙoƙarin bayyana batutuwan da suke ɗamfare da zamantakewa da al’adu da siyasa waɗanda suka jiɓanci yadda ake kallon nakasa da nakasassu. Ita kuwa karin magana ɗaya ne daga cikin sassan adabin baka da Hausawa ke amfani da ita domin ƙawata zance ya yi armashi. Ke nan, karin magana zance ne a dunƙule mai faffaɗar ma’ana, ƙunshe da sharhi kan rayuwar al`umma cikin hikima da fasaha. Shi ya sa karin magana ya zama rumbun ajiye al`adu…
Read More
Gawar Gloria da Linus!

Gawar Gloria da Linus!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Jinjina ga da jami’an tsaro da su ka yi kukan kura zuwa muguwar tungar ’yan ta’addan IP0B a jihar Imo inda hakan ya kai ga gano kabarin da a ke kyautata zaton nan ne a ka binne sojojin nan biyu Warrant Office Linus Audu da Private Gloria Mathew wadanda mugayen irin su ka kashe a shekara ta 2022 lokacin da su ke kan hanyar zuwa ɗaura musu aure a al’adance. A lokacin kisan, mugayen ’yan IP0B da ’yan bindiga daɗinsu ESN sun kashe sojojin da yin gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu, kuma har da naɗar ta’addancin a…
Read More
2027: ADC ta rubuta wasiƙa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya don gaggauta hukunci kan rigimar shugabancin jam’iyyar

2027: ADC ta rubuta wasiƙa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya don gaggauta hukunci kan rigimar shugabancin jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban INEC Amupitan na kitsa maƙarkashiyar murkushe duka jam’iyyun banda APC kadai, muna kira da a tsige shi – ADC Jam’iyyar ADC ta rubuta saƙo zuwa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun, inda ta buƙaci da ta sa baki wajen gaggauta yanke hukunci kan rikicin shugabanci da jam’iyyar da ke gaban kotun ƙoli. A cikin wasiƙar da aka aike wa da ofishin alƙalin alƙalan a ranar Talata, lauyan ADC, S. E. Aruwa (SAN), ya ce, ci gaba da jan ƙafa da aka samu ka iya jefa jam’iyyar cikin halin rasa damar shiga a…
Read More
Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero

Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Alhaji Ado Bayero shi ne Sarki na 55 a jerin sarakunan Kano kuma sarki na 13 a sarakunan Fulani. Tun daga farkon sarautar Kano zuwa shekarar 2017, marigayi Alhaji (Dr.) Ado Bayero shi ne sarkin da ya fi kowane sarki daɗewa a kan karagar mulkin Kano. Sarki ya mulki Kano na tsawon shekaru 51 tun daga 1963 har zuwa 2014. Tsohon ma’aikacin banki, wakilin doka, ma’aikacin hukumar En’e (NA), kuma tsohon wakilin Nijeriya a ƙasar Sinigal. Daraja, da martabar masarautar Kano ta ɗaukaka a iya tsawon mulkinsa. Haihuwarsa: An haifi Alhaji (Dr.) Ado Bayero a ranar…
Read More
Dabarun zama da miji mai saurin fushi da hanyoyin rage masa zafin rai

Dabarun zama da miji mai saurin fushi da hanyoyin rage masa zafin rai

Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D Wannan bincike ya yi nazari kan matsalar saurin fushi a tsakanin maza a cikin aure da kuma rawar da mace za ta taka wajen rage wannan hali. An tattauna dalilai, illoli da hanyoyin magance matsalar ta fuskar ilimin halayyar ɗan’adam da kuma koyarwar addini. Sakamakon ya nuna cewa sadarwa mai kyau, haɗuri da taimakon juna na iya rage wannan matsala sosai. Gabatarwa: Aure wata muhimmiyar alaƙa ce da ke buƙatar fahimta da haɗin kai. Duk da haka, matsaloli irin su saurin fushi na iya kawo tangarɗa ga zaman lafiya. Masana sun nuna cewa rashin…
Read More
Zargin kamfanin Lafarge da tallafa wa ta’addanci ya jawo ayoyin tambaya kan ayyukansa a Nijeriya

Zargin kamfanin Lafarge da tallafa wa ta’addanci ya jawo ayoyin tambaya kan ayyukansa a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukuncin da wata kotu a ƙasar Faransa ta yanke kan kamfanin siminti na Lafarge ya sake tayar da muhawara mai zafi, musamman a Nijeriya, inda kamfanin ke da manyan ayyukan masana’antu duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta na tsawon lokaci. Rahotanni sun nuna cewa, kotu a birnin Paris ta samu kamfanin da laifin tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta hanyar reshensu na Siriya, inda aka ce sun biya kuɗaɗen kariya ga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai domin ci gaba da ayyukansu tsakanin shekarun 2013 da 2014.  Wannan hukunci ya zama tarihi domin shi ne karo…
Read More