Hukumar Abuja za ta rusa gidaje 200 don gina filin saukar jirgin shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya umurci daraktan sashen kula da cigaban ƙasa da ya tabbatar da cewa al’ummar Nuwalege da ke kan titin filin jirgin sama sun ba da fili don gina filin saukar jirgin shugaban ƙasa.

Umarnin ya biyo bayan buqatar da rundunar sojin saman Nijeriya ta gabatar.

Da ya ke magana ta bakin Daraktan, Mukhtar Galadima yayin wani taron al’umma da ’yan ƙasa a ranar Talata a Abuja, Ministan ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi al’umma su ba da damar cigaba.

A cewarsa, “Kimanin wata guda da ya gabata ne hukumar sojin saman Nijeriya ta rubuta wa mai girma minista takarda kan buƙatarsu da kuma buaatar son wannan ƙauyen, domin yana daga cikin shirye-shiryen rundunar shugaban ƙasa.