Daga UMAR GARBA a Katsina
Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta tallafa wa ɗaliban jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma da aka kuɓutar daga hannun ‘yan ta’adda.
Oluremi Tinubu ta bayar da tallafin ne lokacin da ta karɓi baƙuncin huɗu daga cikin ɗalibai biyar na jami’ar.
Babbar mai taimaka wa uwargidan shugaban ƙasar ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi, ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta saka wa hannu.
Kowace yarinya ta samu tallafin karatu Naira milyan ɗaya da sabuwar kwamfutar tafi da gidanka.
Tun farko Shugaba Tinubu ya bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta bai wa iyayen kowace ‘yan matan da aka ceto kuɗi Naira milyan biyu da kuma wata milyan ɗaya ga shugaban jami’ar.
Sanata Oluremi ta kuma ce, ilimi shi ne babbar hanyar yaƙi da matsalar tsaro a Nijeriya.
Daga nan sai ta nuna godiyarta ga jami’an tsaro da suka yi aikin ceto ‘yan matan tare da kira ga ɗaliban da kada su bari abinda ya faru ya kashe musu guiwar neman ilimi.
Blueprint Manhaja ta kawo labarin yadda ɓarayin daji suka sace ɗaliban kimanin watanni biyu da suka wuce.
Rahotanni sun bayyana cewar an kuvutar da ɗaliban ne sakamakon aikin haɗin guiwa tsakanin jami’an tsaro ƙarƙashin kulawar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro.
