Rahoto

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da ta jama’a cikin hatsari a kullum. Direbobin motoci masu zaman kansu, masu kabu-kabu, musamman ’yan J5, Golf da Hiace. Masu adaidaita sahu da masu babur, musamman matasa. Da…
Read More
Waye Ibrahim Taiwo?

Waye Ibrahim Taiwo?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An haifi Ibrahim Taiwo a shekarar 1940, a ƙaramar hukumar Wushishi ta Jihar Neja da ke tarayyar Nijeriya. (Bincikenmu bai samo rana wata da kuma kwanan watan da aka haife shi ba). Ya taso a garin Kagara, har ma a lokacin da ya ke makaranta a kan kirashi da suna Ibrahim Kagara. Ya yi Firamare ɗinsa a Senior Primary School Minna, sai kuma Bida Middle School. Ya halarci Proɓincial Secondary School da ke Okene na ɗan wani taƙaitaccen lokaci, inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare. Aikin Soja: Ya fara shiga aikin damara ne a shekarar…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen…
Read More
Motsa jiki ma kwalliya ne

Motsa jiki ma kwalliya ne

Daga AISHA ASAS Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne. Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaƙulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan…
Read More
Duniya za ta iya tashi a kowane lokaci 

Duniya za ta iya tashi a kowane lokaci 

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Jiya wani kanina ya yi posting cewa "Nan da shekaru biliyan 5 Duniya za ta tashi in ji masana". To, a gaskiyar lamari ba haka abin ya ke ba. Abinda masana Ilimin sararin samaniya ke hasashe shine cewa Rana, wadda ita ce ginshikin wanzuwar Duniya, a yanzu ta kai rabin shekarunta. Wato an haifi wannan Rana tamu kimanin shekaru biliyan 5 da su ka wuce, kuma za ta iya sake kai wasu shekaru biliyan 5 din kafin ta mutu. Masana sun gane haka ne sakamakon nazarin ragowar makamashin nukiliya da ke ci a Rana, wato tamkar…
Read More
Yadda ƙabilar Toraja ke rayuwa da mamaci a Indonesiya

Yadda ƙabilar Toraja ke rayuwa da mamaci a Indonesiya

A wannan mako, jaridar Blueprint Manhaja ta kewaya duniya inda ta yada zango a ƙasar Indonesiya da ke yankin Asiya. A yau shafin na mu na ‘Al'ajabi’ ya yi tattaki na musamman zuwa yankin Gabas-ta-tsakiya, inda za mu yi nazari a kan al’adar ƙabilar Toraja. Wani abu mafi ɗaukar hankali ta yadda har idon duniya ya ɗarsu a kan waɗannan al’umma shi ne yadda su ke tafiyar da sha’anin gawa ko kuma mu ce mamaci. Su dai waɗannan mutane suna rayuwa ne a cikin duwatsun da ke Kudancin Sulawesi ta ƙasar Indonesiya, Kalmar ‘Toraja’ ta samo asali daga yaren ‘Buginese’…
Read More
Tsaro zai inganta a Nijeriya bayan zaɓen 2027 — Akpabio

Tsaro zai inganta a Nijeriya bayan zaɓen 2027 — Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawa, Godswil Akpabio, ya bayyana cewa yanayin tsaro a Nijeriya zai inganta bayan zaɓen 2027 da makonni biyu. Akpbabio ya bayyana haka ne a yayin bikin ƙaddamar da ofshin Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (NRS) a Abuja, inda ya danganta matsalar tsaro da ta yi kamari a ƙasar a halin yanzu da kusantowar zaɓen 2027. Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana gudanar da mulki cikin nagarta, inda ya zargi masu adawa da gwamnati da ɗaukar nauyin tada rikice-rikice a ƙasar. Akpabio ya ce matsalar tsaro tana karuwa ne saboda zaɓen da…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu…
Read More
Tarihin Masarautar Dutse

Tarihin Masarautar Dutse

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A wannan mako Blueprint Manhaja ta taɓo kaɗan daga cikin tarihin fitaccen Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa. Garin Dutse wanda a baya ake fi sani da Dutse Gadawur shi ne sabon sunan garin Garu wanda ya samu a cikin ƙarni na 13 sakamakon zuwan wani maharbi Babarbare mai suna Duna Magu. Tun kafin bayyanar wannan maharbi a wurin, akwai mutane da ke zaune a wannan yanki na Garu da ya koma Dutse daga baya: Wannan gari na Garu, shi ne matsungunin fadar Masarautar Dutse. Tun kusan ƙarni na ɗaya ake kyautata zaton mutane sun zauna…
Read More
Barazanar da ke fuskantar bazawara bayan mutuwar aure 

Barazanar da ke fuskantar bazawara bayan mutuwar aure 

Tare da BILKISU YUSUF ALI Mata da dama sukan shiga matsananciyar damuwa yayin da aurensu ya mutu ko da suna da hannu a mutuwar auren nasu ko kuma tsautsayi ya rutsa da su ko ganganci. A yau, Bazawara ba a  tunanin ina matsalarta take mene dalili maimakon haka ƙazafi da sharri da kallon banza da tsangwama shi ne zai biyo baya in har ba a yi sa’a da dace ba ana kallo a unguwa sai ta faɗa mummunan yanayi ba mai taimaka mata. Mace ba ita kaɗai ce ke da alhakin riƙe aure ba, hasali ma ita sakin ba a…
Read More