Tsaro zai inganta a Nijeriya bayan zaɓen 2027 — Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswil Akpabio, ya bayyana cewa yanayin tsaro a Nijeriya zai inganta bayan zaɓen 2027 da makonni biyu.

Akpbabio ya bayyana haka ne a yayin bikin ƙaddamar da ofshin Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (NRS) a Abuja, inda ya danganta matsalar tsaro da ta yi kamari a ƙasar a halin yanzu da kusantowar zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana gudanar da mulki cikin nagarta, inda ya zargi masu adawa da gwamnati da ɗaukar nauyin tada rikice-rikice a ƙasar.

Akpabio ya ce matsalar tsaro tana karuwa ne saboda zaɓen da ke tafe, amma nan da makonni biyu bayan kammala zaɓe za ta ragu.

Ya kuma yi ba’a ga ’yan adawa, musamman dan takarar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, inda ya ce, “’yan adawa sun shiga rudani. Mutumin da ya samu kuri’u milyan shida ya sauya sheka daga jam’iyyar, yana zargin jam’iyya mai mulki.”

Akpabio ya roƙi ’yan Nijeriya da su yi haƙuri da gwamnatin Tinubu.

A wajen bikin ƙaddamar da sabon ginin hukumar haraji, Akpabio ya yi kirari ga shugaban hukumar, Dakta Zacch Adedeji, a yayin bikin, wanda ya samu halarcin mnayan jami’an gwamnati ciki har da Shugaba Bola Tinubu da ya kaddamar da ginin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Jibrin Barau, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da Mataimakin Kakakin Benjamin Kalu.

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu, ministoci, da kuma gwamnoni daga jihohi daban-daban.

Gwamnonin da suka halarta sun hada da Babagana Zulum (Borno), Charles Soludo (Anambra), Caleb Mutfwang (Filato), Hope Uzodimma (Imo), da kuma Usman Ododo (Kogi).

Sabon ginin hukumar haraji da aka kaddamar, wanda aka bayyana a matsayin gini na zamani, yana da bene 16 tare da damar daukar ma’aikata kusan 3,000.

A watan Yuni 2025 ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS), wacce ta maye gurbin FIRS.

By ukarofi